Masu sharhi a harkokin siyasa sun jinjina wa Shugaba Lazarus Chakwera bisa naɗa mataimakin shugaban jam'iyyar su  Saulos Chilima a matsayin sabon mataimakin shugaban Malawi./Hoto:AFP

Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya naɗa Ministan Albarkatun Ƙasa Michael Bizwick Usi a matsayin sabon mataimakin shugaban ƙasar, domin maye gurbin Saulos Chilima, wanda ya mutu a makon jiya sakamakon hatsarin jirgin sama.

Usi fitaccen marubuci ne kuma ɗan wasan kwaikwayo wanda kuma yake kare hakkin ɗan'adam da yin sharhi kan lamuran yau da kullum. Shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar United Transformation Movement (UTM) ta su Chilima tun da aka kafa ta a 2018.

Ya shiga gwamnatin Chakwera a 2020 lokacin da jam'iyyar UTM ta ƙulla ƙawance da jam'iyyar su Chakwera mai suna Malawi Congress Party (MCPP) a zaɓukan da aka gudanar a 2020.

Usi, mai shekara 56, yana da digirin Masters a fannin tsare-tsare da ci-gaba. Kazalika ya yi digirin digirgir a fannin ci-gaban matasa.

Kafin ya shiga harkokin siyasa, Usi ya yi aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu na ci-gaban al'umma.

An rantsar da shi ranar Juma'a a matsayin sabon mataimakin shugaban Malawi a Lilongwe, babban birnin ƙasar.

Chilima ya mutu ne sakamakon hatsarin da wani jirgin sojoji da ke ɗauke da shi da wasu mutum tara ya yi a Gandun Dajin Chikangawa da ke birnin Mzuzu a arewacin ƙasar sakamakon rashin kyawun yanayi.

TRT Afrika