Daga Coletta Wanjohi
Hukumar Yaki da dakile yaduwar cutuka ta Afirka ta ce cutar kwalara na raguwar a Malawi.
Abinci ko ruwan da ya gurbuta da cutar Vibrio cholera ke haddasa cutar.
A makon da ya gabata, mutane 3.694 ne suka kamu da cutar inda mutum 76 suka rasa rayukansu. Hukumar lafiya ta nahiyar ta ce a mako hudu da suka wuce an samu raguwar cutar sosai.
“Yaduwar cutar na raguwa saboda agajin da gwamnati tare da taimakon hukumar yaki da cututa ta Afirka ke bayarwa in ji Ahmed Ogwell, mukaddashin shugaban Africa CDC.”
“Hanyoyi mafiya muhimmanci na dakile cutar su ne tsabtace ruwan da ake amfani da shi da kuma hana gaurayar ruwan da ke fita daga jikin dan Adam.”
Malawi na daga cikin kasashe 14 na Afirka da ke fama da annobar kwalara a yanzu.
Abin da ya kamata ku sani game da kwalara a Kudancin Afirka
Kasashen da abin ya shafa su ne Malawi da Mozambique da Afirka ta Kudu da Zambia da kuma Zimbabwe.
A Malawi mutane 53,660 ne suka kamu da cutar inda 1,652 suka rasu tun da annobar ta barke a Fabrairun 2022.
Guguwar da ta auku a Fabrairun 2023 ta haddasa ambaliyar ruwa a Malawi da kuma Mozambique inda ta lalata wuraren kiwon lafiya.
A Zambia mutum 225 ne suka kamu da cutar izuwa yanzu. Kasancewar akwai kasuwa kusa da iyakar Malawi ka iya kara yawanta a kasar.