Wani jirgi mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a kusa da kauyen Chukuba na Jihar Neja da ke arewacin kasar.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe daya na rana a agogon Nijeriya a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar da daraktan watsa labaran rundunar sojin saman, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar ta bayyana.
"Helikwaftan yana kan hanyarsa ta tafiya Kaduna ne bayan da ya bar Makarantar Firamare ta Zungeru inda daga baya aka gano ya fadi a kauyen Chukuba da ke karkashin karamar hukumar Shiroro," kamar yadda sanarwar ta ce.
Rundunar ba ta bayar da rahoton ko an rasa rayuka a hatsarin ba, amma ta ce ana aikin ceto matukan jirgin da fasinjojin da ke cikinsa, sannan an kaddamar da binciken farko don gano musabbabin hatsarin.