Shugaban Kenya William Ruto ya sauke dukkan ministocinsa daga kan muƙamansu ban da na Harkokin Ƙasashen Waje, kwanaki kaɗan bayan an gudanar da jerin zanga-zanga a ƙasar.
Shugaba Ruto ya sanar da sauke ministocin daga kan muƙamansu ne a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Alhamis.
Babu abin da ya shafi Ofishin Mataimakin shugaban ƙasa amma an an sallami antoni janar na ƙasar
Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ya yi "tunani, sannan mun saurari abubuwan da 'yan ƙasar Kenya suke buƙata da kuma duba nasarori da ƙalubalen gwamnatina".
"Nan-take zan soma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban da kuma 'yan siyasa, da zummar kafa gwamnatin da za ta ƙunshi kowa da kowa," in ji shi.
Ruto ya ce za a ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati ba tare da fuskantar tsaiko ba inda manyan sakatarori da jami'an gwamnati za su jagoranci tafiyar da lamura.