Shugaba Umaro Sissoco Embalo, wanda aka zabe shi a watan Disamba na 2019 don yin wa'adin shekara biyar a mulki, ya je  Dubai don halartar taron COP28 kan sauyin yanayi lokacin da lamarin ya faru./Hoto:OTHER

Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce yamutsin da aka yi a babban birnin kasar tsakanin sojoji da Runduna ta Musamman da ke fadar shugaban kasa a ranar Alhamis wani "yunkurin juyin mulki" ne.

Embalo, wanda ya je Dubai don halartar taron COP28 kan sauyin yanayi, ya ce ya kasa komawa kasarsa ne nan-take "saboda an yi yunkurin juyin mulki. Ina so na shaida muku cewa za a dauki mataki mai tsauri kan wadanda suka haddasa wannan lamari", in ji shugaban kasar yayin da ya koma Bissau ranar Asabar.

Rundunar sojin Guinea-Bissau ta umarci Dakaru na Musamman su koma bariki, bayan yamutsin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum biyu wanda ECOWAS ta yi Allah wadai da shi.

Ranar Alhamis da daddare rikici ya barke tsakanin sojojin Dakaru na Musamman na Kasa da kuma Runduna ta Musamman da ke tsaron fadar shugaban kasa a Bissau babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

Wani babban jami'in soji, wanda ba ya so a ambaci sunansa saboda sarkakiyar lamarin, ya ce sojoji shida sun jikkata kuma an kai su makwabciyarsu Senegal.

Hankula sun kwanta ranar Juma'a da rana a kasar da ta yi kaurin suna wurin tashin hankali, bayan an bayar da sanarwa cewa sojoji sun kama Kanar Victor Tchongo, kwamandan Dakaru na Musamman na Kasar.

Ranar Asabar an rage yawan jami'an tsaro a kan titunan Bissau, amma an ga sojoji jibge a wasu wurare na musamman da suka hada da fadar shugaban kasa da ma'aikatar shari'a da wasu ma'aikatu.

TRT Afrika da abokan hulda