Mista Mahama ya gargaɗi ministocin nasa da sauran masu riƙe da muƙamai da su guji wadaƙa da kuma rayuwa mai tsada. / Hoto: Reuters

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya bayar da umarni ga duka ministocinsa da jami’an gwamnati kan su daina amfani da kujerun jirgi mafi a lokacin tafiye-tafiye, duk a yunƙurin rage kashe kuɗi.

Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da yake rantsar da ministoci 17 da ya naɗa.

Mista Mahama ya yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani jami'i da aka kama yana almubazaranci da dukiyar al'umma ko kuma aikata cin hanci.

“Na buƙaci shugaban ma’aikata ya rubuta wasiƙa ga dukkan masu riƙe da muƙamai kan cewa na haramta tafiye-tafiye waɗanda ba su da muhimmanci domin rage kashe kuɗi,” kamar yadda ya bayyana.

Haka kuma ya gargaɗi ministocin nasa da sauran masu riƙe da muƙamai da su guji wadaƙa da kuma rayuwa mai tsada.

Mista Mahama ya ce akwai buƙatar masu riƙe da muƙamai su riƙa girmama mutanen Ghana domin su suka zaɓe su.

Ya bayyana cewa kuɗin da ake amfani da su na mutanen Ghana ne kuma bai kamata a rinƙa ɓarnata su ba.

TRT Afrika da abokan hulda