Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya soke dukkan tafiye-tafiyen jami'an gwamnati, ciki har da shi kansa, zuwa kasashen waje a wani mataki na rage kashe kudaden gwamnati, kamar yadda kakakin gwamnati ya bayyana ranar Asabar.
Barrow ya sanya hannu a kan dokar shugaban kasa wadda ta "dakatar da shugaban kasa da mataimakinsa da ministoci da manya jami'an gwamnati da ma'aikatan gwamnati da kuma dukkan ma'aikatan hukumomi" daga tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a sauran watannin da suka rage a wannan shekarar, a cewar mai magana da yawunsa Ebrima Sankareh a sanarwar da ya fitar.
Sai dai za a bar jami'an su halarci tarukan da suka zame wa Gambia wajibi sannan za a kyale su su tafi kasashen waje idan ba gwamnati ce za ta dauki nauyin biyan kudin tafiye-tafiyen ba.
Gambia, kasar da ta fi kankanta a nahiyar Afirka mai yawan jama'ar da bai wuce mutum miliyan biyu da 'yan kai ba, ita ce ta 174 cikin kasashe 191 a kididdigar ci-gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta hada da kiwon lafiya, ilimi da tsarin rayuwa.
Bankin Duniya ya ce mutum daya cikin biyar na 'yan kasar yana rayuwa da abin da bai kai dala biyu ba. Hauhawar farashi ta kai kashi 11.6 cikin dari a kasar a bara.
A yayin da kasar ke fama rashin isasshen haraji, sannan take bayar da tallafi a kan fetur da takin zamani da kuma hatsi sakamakon yakin da ake yi a Ukraine, kasafin kudinta ya karu a shekarar da ta wuce.
An kara samun gibi a kasafin kudin kasar da kuma karuwar bashi a kanta, a yayin da aka samu raguwar haraji.