Fasfo wani muhimmin abu ne da shi ne babban abin da matafiyi ke bukata don shiga wata kasar. Hoto: Getty Images      

Daga Brian Okoth

Fasfo din kasar Seychelles shi ne mafi karfi a Afirka, daga shi sai na Mauritius da Afirka ta Kudu.

Wannan abu na zuwa ne bayan fitar rahoton cibiyar Henley Passport Index, wata hukuma mai kula da harkokin shige da fice da ke Landan, wacce ta fitar da jerin karfin fasfunan kasashen duniya bisa duba da yawan kasasen da mai rike da su zai iya shiga ba tare da samun biza gabanin tafiyar ba.

Fasfo wani muhimmin abu ne da shi ne babban abin da matafiyi ke bukata don shiga wata kasar.

Baya ga dimokuradiyya da karfin siyasa da tsaro da taimakekeniya, cibiyar Henley & Partners ta ce kudaden shiga ma wani muhimmin abu ne da ake la'akari da shi wajen gane karfin fasfo.

"Kasashen da suke da karfin ma'aunin tattalin arziki kamar yadda bayanan Bankin Duniya suka fayyace ma suna morar shiga kasashe da dama ba tare da biza ba," a cewar cibiyar.

Fasfo din kasar Seychelles ka iya bai wa mai rike da shi damar shiga kasashe 155 a fadin duniya ba tare da biza ba. Kasar ce ta 24 a jerin kasashen duniya masu karfin fasfo.

Seychelles, wacce ke da yawan al'umma kusan 100,000, wani tsibiri ne da ke kan Tekun Indiya. Hoto: AA

Seychelles, wacce ke da yawan al'umma kusan 100,000, wani tsibiri ne da ke kan Tekun Indiya, a kusa da Gabashin Afirka. Waje ne da ke da tarin gabobin teku da kyawun yanayi.

Mauritius, ita ma wata kasar da take kan tsibiri a Gabashin Afirka, ita ce ta 29 a jerin kasashen duniya mafiya karfin fasfo, inda ake iya zuwa kasashe 148 a fadin duniya ba tare da biza ba.

Fasfon Afirka ta Kudu ne na uku a nahiyar

Fasfon Afirka ta Kudu yana bai wa masu rike da shi damar shiga kasashe 106 a duniya ba tare da biza ba, in da hakan ya sa ya zama na uku mafi karfi a Afirka. Sannan fasfon Afirka ta Kudu shi ne na 52 mafi karfi a duniya.

Botswana ce kasa ta 60 mafi karfin fasfo a duniya, inda masu rike da shi ka iya shiga kasashe 89 babu biza. A Afirka kuwa shi ne ya zo na hudu.

Fasfon kasar Namibiya na bai wa masu rike da shi damar zuwa kasashe 80 a duniya, in da ya zama na 64 a duniyar da kuma na biyar a Afirka. Fasfon Namibiya yana da alaka da na China da Saudiyya da kuma Bolivia.

Lesotho, wacce take daya daga cikin kasashen Afirka da ba su da girman kasa, fasfonta na da karfin da ke bai wa mai rike da shi damar shiga kasashe 79 a duniya. Karfin fasfonta a jerin kasashen duniya ya zo daya da na Thailand a mataki na 65, A Afirka kuwa ita ce ta shida.

Wata kasar da ke yankin Kudancin Afirka wato Eswatini ma fasfonta ya kasance na bakwai mafi karfi a Afirka, sannan na 67 a duniya, inda yake bai wa mai rike da shi damar shiga kasashe 77.

Kasar Kenya da ke gabashin Afirka ce ta takwas a nahiyar a karfin fasfo, ta kuma zama ta 68 a duniya in da ake iya zuwa kasa 76 da shi ba tare da biza ba.

Malawi da Tanzania ne suka cike teburin kasashe 10

Fasfon Malawi yana bayan na Kenya a matsayi a nahiyar Afirka sannan shi ke bin bayan na Kenyan dai a duniya - wato na tara a Afirka sannan na 69 a duniya in da yake bai wa masu rike da shi damar zuwa kasashe 79 a duniya babu biza.

Makwabciyar Kenya Tanzania ce kasa ta 10 a Afirka da fasfonta ya fi karfi. Ana iya zuwa kasashe 73 na duniya da fasfon Tanzania ko babu biza, hakan ne ya sa ta zama kasa ta 70 a jerin kasashen duniya masu karfin fasfo.

Ga dai jerin kasashe 20 da suka fi karfin fasfo a Afirka a takaice:

  1. 1. Seychelles: ta 24 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 155
  2. 2. Mauritius: ta 29 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 148
  3. 3. South Africa: ta 52 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 106
  4. 4. Botswana: ta 60 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 89
  5. 5. Namibia: ta 64 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 80 (alaka da China da Saudiyya da Bolivia)
  6. 6. Lesotho: ta 65 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 79 (alaka da Thailand).
  7. 7. Eswatini: ta 67 a duniya– kasashen da za a iya zuwa ba biza 77 (alaka da Kazakhstan)
  8. 8. Kenya: ta 68 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 76
  9. 9. Malawi: ta 69 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 75
  10. 10. Tanzania: ta 70 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 73
  11. 11. Tunisia, Zambia: na. 71 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 71
  12. 12. Gambia: ta 72 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 70
  13. 13. Uganda: ta 73 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 69
  14. 14. Moroko da Saliyo da Zimbabwe: ta 74 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 67
  15. 15. Cape Verde: ta 75 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 66 (alaka da Philippines)
  16. 16. Ghana: ta 76 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 65
  17. 17. Mozambique da Rwanda: na 77 a duniya – kasashen da za a iya zuwa ba biza 63

Sai dai fasfunan manyan kasashen Afirkan biyu Nijeriya da Masar ba su kasance cikin 20 din farko mafiya karfi ba a Afirka, don kuwa kasashen da ake iya zuwa a fadin duniya babu biza da fasfunan ba su wuce 60 ba.

Ana iya zuwa kasashe 46 ne kawai ba tare da biza ba da fasfon Nijeriya, kuma yana mataki na 91 a duniya, inda suke daidai da fasfon Sudan ta Kudu.

Shi kuwa fasfon kasar Masar na bayar da damar zuwa kasashe 54 babu biza, sannan shi ne na 84 a duniya. Masar tana kan mataki daya da Chadi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Comoros da kuma Aljeriya.

Singapore ce kan gaba a duniya

Fasfon kasar Singapore shi ne mafi karfi a duniya. Yana ba da damar shiga kasashe 192 cikin 227 na fadin duniya ba tare da biza ba. Jamus da Italiya da Sipaniya su ne suka yi kunnen doki a matsayin na biyu, inda fasfunansu ke ba da damar zuwa kasashe 190 bbau biza a duniya.

Fasfion Singapore na ba da damar shiga kasashe 192 cikin 227 na fadin duniya ba tare da biza ba. Hoto: AA

Kasashen Austria da Finland da Faransa da Japan da Luxembourg da Koriya ta Kudu da Sweden sun yi kunnen doki a matsayin na uku inda za a iya zuwa kasa 189 da fasfunansu a duniya ba tare da biza ba.

Fasfon Birtaniya na da karfin da za a iya zuwa kasashe 188 da shi babu biza, lamarin da ya sa ya zama na hudu a duniya shi da na Netherlands da Denmark da kuma Ireland.

Amurka, wacce kusan ita ta fi kowacce kasa karfin fada a ji a duniya, ga mamaki fasfonta shi ne na takwas a mafiya karfi, in da suka zo daidai da na Lithuania, ana iya shiga kasashe 184 da fasfunansu ba tare da biza ba a duniya.

"An samu wannan jeri ne bisa ga bayanan da aka tattara daga Hukumar Sufurin Jiragen Sama da Kasa da Kasa (IATA), wacce ita ce hukuma mafi girma da take da sahihan bayanai da kamfanin Henley & Partners suka yi aiki da bayanansu," kamar yadda cibiyar Henley & Partners ta fada a wata sanarwa.

"Babban abin da ake dubawa tsawon shekara 18 a fitar da jerin shi ne duba kan 'yancin tafiye-tafiye in da kuma yawan kasashen da matafiya za su iya zuwa ba tare da biza ba ya ninka daga 58 a 2006 zuwa 109 a 2023," Henley & Partners ta kara da cewa.

Cibiyar mai mazauni a Landan ta gano cewa tazarar da ke tsakanin kasashen da ke can saman jerin da wadanda suke kasa tana da yawa sosai fiye da yadda ta saba kasancewa.

“Singapore wacce fasfonta ke ba da damar shiga kasashe 165 babu biza suna da matukar yawa fiye da na Afghanistan wacce ita ce ke can kasa a jerin,” in ji Henley & Partners.

TRT Afrika