Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta dage haramcin bayar da biza da ta sanya wa 'yan Nijeriya.
Haramcin, wanda ya kai tsawon wata 10, ya shafi al'amuran 'yan Nijeriya da dama da suke yawan zuwa kasar UAE don harkokinsu na kasuwanci ko yawon bude ido.
A wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Nijeria Bola Tinubu kan watsa labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce UAE ta dage haramcin ne bayan ganawar da Tinubu ya yi da shugaban kasar UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan a ranar Litinin.
"An cimma yarjejeniya mai dimbin tarihi da ta jawo dage haramcin ba da biza da aka saka wa matafiya 'yan Nijeriya ba tare da bata lokaci ba," in ji sanarwar.
Sannan kuma bisa wannan yarjejeniyar, kamfanin jiragen Etihad da Emirates za su fara jigila a ciki da wajen Nijeriya ba tare da wani bata lokaci ba.
“Gwamnatin Nijeriya ba ta biya ko sisi ba a sasantawar da aka yi tsakanin shugabannin kasashen biyu da dawo da harkokin sufuri na wadannan kamfanonin jirage biyun da kuma tsakanin kasashen biyu,” in ji sanarwar.
Sabbin zuba jari
Baya ga batun janye haramcin biza, sanarwar ta kuma ce bisa tsarin ci gaban tattalin arziki na Shugaba Tinubu, “a yau ya gabatar da wani shiri da aka amince da shi, inda zai kunshi sabbin zuba jari na biliyoyin daloli a tattalin arzikin Nijeriya a fannoni daban-daban da suka hada da tsaro da noma da sauran su.”
“Sannan kuma Shugaba Tinubu ya yi farin cikin yana farin cikin sanar da cimma wata yarjejeniya ta wani sabon shirin samar da kudaden kasashen waje tsakanin gwamnatocin biyu, wanda za a sanar da cikakken bayani a kansa nan da makonni masu zuwa.”
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa shugaban UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan kan kyakkyawan kawancen da yake nunawa da jajircewarsa wajen hada hannu don farfado da dangantakar kasashen biyu.