Azali Assoumani ya taba rike mukamin shugaban kasar Comoros a lokuta da dama. / Hoto: Reuters      

A karon farko, shugaban Comoros Azali Assoumani ya bayyana a ranar Alhamis don jagorantar taron Majalisar Ministocin Gwamnatin bayan raunin da ya ji a wani harin wuƙa da aka kai masa a makon jiya.

Bidiyon da fadar gwamnatin ƙasar ta wallafa ya nuna Azali sanye da wani bandeji mai kauri a gefen goshinsa na hagu, yana murmushi yayin da yake ƙoƙarin shiga mota da kuma isa fadar Shugaban Ƙasa, inda ya gaisa da ministocinsa da sauran manyan jami'ai masu ba shi shawara kafin ya samu wurin zama da aka yi masa tanadi.

Shugaban dai ya ɗan jikkata a harin wuƙa da aka kai masa a ranar Juma'a a yayin taron jana'izar wani fitaccen malamin addini a Salimani Itsandra, wani gari da ke yankin arewa da Moroni babban birnin ƙasar.

Bayan harin ne aka tsinci gawar maharin a gidan yari ba tare da sanin dalilin mutuwarsa ba, kamar yadda lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara ya bayyana a ranar Asabar.

TRT Afrika