Mista Masra na daga cikin manyan 'yan adawa a kasar Chadi a baya. / Hoto: Others

Shugaban mulkin soja na Chadi Mahamat Idriss Deby Itno a ranar Litinin ya nada tsohon shugaban ‘yan adawa na kasar a matsayin Firaiminista.

An nada Mista Succes Masra a matsayin firaiminista jim kadan bayan dawowarsa daga gudun hijirar da ya yi.

Mista Masra wanda shi ne shugaban Jam’iyyar Transformers, ya kasance dan adawa tun zamanin Marigayi Idriss Déby, sai dai ya koma Chadi a watan Nuwamba bayan ya cimma matsaya da shugabannin mulkin sojin kasar.

Nadin sabon firaiministan na zuwa ne mako guda bayan an amince da sabon kundin tsarin mulki a kasar ta Chadi bayan an gudanar da zaben raba gardama kan hakan.

‘Yan adawa sun ta sukar zaben inda suka rinka cewa wannan wata hanya ce ta sharar fage ga shugaban mulkin sojin kasar Janar Mahamat Idriss Deby Itno domin zama shugaban kasar.

Kuri’ar raba gardamar da aka gudanar wani muhimmin mataki ne na mayar da mulki ga farar hula kafin karshen shekarar 2024, kamar yadda shugabannin sojin kasar suka yi alkwari.

TRT Afrika