Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabbin ministocinsa bayan Majalisar Dattawan kasar ta tantance su.
Ranstuwar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da shugaban ya sanar da ma’aikatun da sabbin ministocin za su yi aiki, inda a ranar Lahadin da ta gabata ya sake wasu sauye-sauye kan wasu ministocin.
An soma gudanar da taron rantsuwar ne da misalin karfe 10:00 na safiyar Litinin a babban dakin taro na Fadar Shugaban Nijeriya da ke Abuja.
Mutum biyar-biyar aka rantsar a lokaci daya, inda kafin su sha rantsuwar sai da aka rinka karanto takaitaccen tarihinsu.
Ministocin farko da suka soma shan rantsuwar sun hada da Lateef Fagbemi a matsayin Ministan Shari’ar na kasa sai Ekperipe Ekpo a matsayin Ministan Albarkatun Gas.
Haka kuma akwai Nkiruka Onyejeocha a matsayin Ministan Kwadago da Ayyukan Yi sai kuma Uju Kennedy a matsayin Ministar Harkokin Mata da Tahir Mamman a matsayin Ministan Ilimi.
Labari mai alaka: Badaru da Matawalle a ministocin tsaro: Shin an ajiye kwarya a gurbinta?
Tun da farko nadin ministocin ya jawo ce-ce-ku-ce kan abubuwa da dama a kasar. Jim kadan bayan Shugaba Tinubu ya fitar da sunayen ministocinsa a karo na biyu wanda a ciki akwai Maryam Shettima wadda aka fi sani da Maryam Shetty, sai aka sauya sunanta da Mairiga Mahmud.
Wannan lamari ya matukar jawo ce-ce-ku-ce a Nijeriya. Haka kuma bayan da Majalisar Dattijan Nijeriya ta ki amincewa da sunan Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a matsayin minista, shi ma ya zama abin magana inda aka yi ta mayar da martani dangane da lamarin daga fuskoki daban-daban.
Sai kuma na baya-bayan nan shi ne batun raba ma’aikatu da aka yi ga ministocin inda jama’a da dama musamman a shafukan sada zumunta suke korafi kan wasu daga cikin ministocin inda suke cewa ba su dace da ma’aikatun da aka ba su ba.