Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mista Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon shugaban Hukumar Tsaro ta DSS, yayin da ya naɗa Mohammed Mohammed a matsayin sabon shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa NIA.
Mai Bai wa Shugaba Tinubu Shawara na Musamman Kan Kafofin Watsa Labarai Chief Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Oluwatosin zai maye gurbin Yusuf Bichi ne a DSS, yayin da Mohammed Mohammed kuma zai maye gurbin Ahmed Rufai Abubakar a NIA.
A makon da ya gabata ne Shugaban Hukumar NIA Ahmed Rufai Abubakar ya yi murabus, inda shi kuma Bichi ya yi murabus daga DSS a ranar Litinin.
Shugaban Nijeriyar ya buƙaci sabbin shugabannin hukumomin da su yi aiki tuƙuru da kuma amfani da ƙwarewarsu wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta na tsaro.
Haka kuma ya buƙace su su yi aiki kafaɗa da kafaɗa tare da sauran hukumomin tsaro na ƙasar domin yi wa ƙasa aiki.
Naɗin sabbin shugabannin hukomin na DSS da NIA na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassa na Nijeriya.