Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kayyade adadin mutanen da za su rinka masa rakiya zuwa kasashen waje zuwa mutum 20.
Wannan na zuwa ne a yunkurin da shugaban kasar yake yi na rage kashe kudi a kasar.
“A tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, shugaban ya bayar da umarnin kada mutanen da za su raka shi su haura 20. Wannan adadin zai ragu zuwa biyar ga mai dakinsa (Oluremi Tinubu),” kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale ya bayyana a ranar Talata a Abuja.
Shugaba Tinubu ya ce matarsa Oluremi Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima adadin mutanen da za su rinka tafiya da su kasashen waje kada ya wuce mutum biyar.
Haka kuma shugaban ya kayyade adadin mutanen da za su rinka raka shi wurare a cikin Nijeriya zuwa mutum 25.
A bangaren ministoci kuwa, kowane daga cikinsu mutum hudu aka kayyade ya rinka tafiye-tafiye da su zuwa kasashen waje, sai kuma shugaban ma’aikatu mutum biyu kowanensu.
Ngelale ya bayyana cewa shugaban yana matukar kashe kudi a tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen waje sakamakon alawus-alawus da kuma kudaden kashewa da ake bai wa ‘yan rakiyar tasa.