Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gargadi dansa Seyi da wasu mutane da ke fadar shugaban kasar su daina shiga taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya wato FEC.
Shugaban kasar ya bayyana haka a lokacin taron majalisar a ranar Talata.
Mista Tinubu ya ce ya lura dansa Seyi da wasu mutane da ba a amince su shiga taron ba suna shige-da-fice a dakin taron a makon jiya a yayin da ake tattaunawa kan muhimman abubuwa da suka shafi kasar.
Shugaban ya gargade su game da wannan dabi’a tare da yi musu hani da aikata hakan.
Shugaba Tinubu ya lissafo sunayen mutum hudu wadanda ya ce su kadai ya amince su halarci taron bayan ministocinsa.
“A makon da jiya, na lura da wasu mutane suna shige-da-fice a yayin wannan taron, na ga hoton dana Seyi yana zaune a baya. Ba za a yarda da wannan ba. Zan sanar muku mutanen da suka kamata su kasance a nan,” in ji shi.
Shugaban ya ce wadanda ya amince su halarci taron sun hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsare-tsare Hadiza Bala Usman da mai taimaka masa kan bayanai da dabaru Bayo Onanuga da sakatarensa na musamman Hakeem Muri-Okunola da sakatarensa Damilotun Aderemi.
Shugaban ya ce wadannan ne kadai ya amince su zauna a taron sai dai idan shi ya bukaci wani ya shigo taron.
Mista Tinubu ya kuma gargadi Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnati da su kula da abin da ya fada kan wannan lamarin.