Shugaban Nijeriya Bola Tinubu na ci gaba da tuntubar manyan masu ruwa da tsaki kan yadda za a dora tattalin arzikin kasar kan ingantacciyar hanya.
Game da hakan ne, a ranar Laraba shugaban tare da mataimakinsa Kashim Shettima suka gana da shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da wasu gwamnoni da suka hada da na jihohin Imo da Kwara da Lagos da kuma Ogun, kamar yadda gidan talabijin na kasa NTA ya bayyana.
Tattalin arzikin Nijeriya dai yana cikin wani yanayi na tabarbarewa, kamar yadda masana suka tabbatar, inda karyewar darajar naira da har ta haura 800 kan kowace dala da karuwar farashin fetur sakamakon janye tallafin mai da gwamnati ta yi suka hadu suka ta'azzara hauhawar farashi a kasar.
Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ma ya halarci taron da Shugaba Tinubun ya yi kan lalubo bakin zaren inganta tattalin arzikin kasar.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabarun aiki, Dele Alake ya bayyana cewa taron ya tattauna kan yadda za a kawo karshen shirin raba arzikin kasa don rage radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.
A makon da ya wuce ne Fadar Shugaban Kasar ta bayyana shirin raba hatsi da takin zamani ga manoma a matsayin wani bangare na matakan bunkasa samar da abinci a kasar.