Fadar shugaban Nijar ta ce a shirye sojoji da dakaru na musamman suke su kai wa sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa hari./Hoto: Fadar shugaban Nijar

Fadar shugaban kasar Jamhuriyar ta tabbatar da cewa wasu sojojin fadar shugaban kasar sun tayar da yamutsi ranar Laraba.

Ta bayyana haka ne a wasu sakonni da ta wallafa a shafin Twitter na fadar shugaban kasar.

Hakan na faruwa ne a yayin da rahotanni daga kasar ke cewa wasu sojoji da ke kula da fadar shugaban kasar da ke Yamai sun toshe ofishin shugaban kasa da kuma gidansa.

"Ranar Laraba da sanyin safiya, wasu sojoji da ke gadin fadar shugaban kasa sun yi abin da ya saba wa Jamhuriya sannan suka nemi goyon bayan sojojin kasar da dakaru na musamman ko da yake ba su cimma burinsu ba. Shugaban kasa da iyalansa suna nan kalau," a cewar sanarwar.

Ta kara da cewa: "A shirye sojoji da dakaru na musamman suke su kai wa sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa hari wadanda suka yi wannan aiki idan ba su dakatar da aniyarsu ba."

Tun da farko, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na soji suna cewa sojojin run rufe dukkan hanyoyin da ke shiga fadar ta shugaban kasa a ranar Laraba.

Wani wakilin Reuters ya ga motocin soji suna shiga fadar shugaban kasar.

Wani jami'in fadar shugaban kasar ya ce ba a barin ma'aikatan fadar su shiga cikinta.

Kazalika an toshe hanyoyin shiga ma'aikatun da ke kusa da fadar shugaban kasar, a cewar majiyoyin tsaro.

Ba a sani ba ko Shugaba Mohamed Bazoum yana fadarsa ko kuma ba ya nan.

Babu alamar tashin hankali a Yamai da safiyar Laraba yayin da ababen hawa ke kaiwa da komowa kuma mutane na iya amfani da intanet, in ji wakilin TRT Afrika da ke birnin.

An yi yunkurin juyin mulki a kasar Nijar a watan Maris na shekarar 2021, a lokacin da wasu sojoji suka yi kokarin karbe iko da fadar shugaban kasa 'yan kwanaki kafin a rantsar da Bazoum bayan an zabe shi.

Mohamed Bazoum shi ne shugaba na farko na farar-hula da ya karbi gwamnati daga hannun wani shugaban na farar-hula a kasar da aka yi juyin mulki sau hudu tun bayan samun 'yancinta daga Faransa a shekarar 1960.

Reuters