Hayaƙi na tashi saman gine-gine bayan luguden wuta ta sama yayin wani batakashi tsakanin dakarun sojin ƙasar da kuma rundunar ɗaukin gaggawa ta ƙasar a arewacin Khartoum, Sudan. / Hoto: Reuters

Amurka ta nemi duniya ta ƙara nuna kulawa kan batun Sudan, kusan shekara guda bayan da ƙazamin yaƙi ya ɓarke a ƙasar, inda ta bayyana fatan komawa teburin sulhu nan gaba kaɗan.

Jakadar Amurka a Mjalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield ta ce, "Yayin da al'ummomi a Sudan ke fama da yunwa, ga cututtuka irinsu kwalara da ƙyanda da ke yaɗuwa, ga faɗa na ci gaba da saryar da rayuka, duniya ta yi biris da Sudan".

Ta faɗa wa manema labarai a birnin Washington cewa, "Dole wannan ya sauya koma dole sauyin ya fara yanzu. Ya wajaba al'ummar duniya ta ƙara ƙaimi wajen nuna damuwa kan lamarin".

Wata daɗaɗɗiyar tsama tsakanin dakarun sojin ƙasar da kuma rundunar ɗaukin gaggawa ta ƙasar ya haifar da yaƙi ranar 15 ga Afrilun 2023, inda ya haddasa mutuwar dubban mutane, sannan miliyoyi suka yi gudun hijira, kuma ƙoƙarin ƙasar na komawa mulkin farar-hula ya samu tasgaro.

Yanke tallafi

Sai dai yaƙin Gaza da ya zo daga baya cikin shekarar ta 2023 ya kawar da hankali daga yaƙin Sudan.

Thomas-Greenfield ta ce kashi biyar cikin ɗari kacal aka tara a gidauniyar tallafa wa Sudan da MDD ta ƙaddamar don samar da kayan jinƙai, wanda hakan ya haifar da raguwar tallafi ga 'yan gudun hijrar ƙasar.

Ta kuma ce Amurka za ta "ƙara" samar da kuɗi cikin kwanaki masu zuwa. Ranar Litinin Faransa za ta jagoranci taron ƙasa-da-ƙasa kan jinƙai a Sudan.

Jakada na musamman kan Sudan, Tom Perriello, ya bayyana fatansa na amfani da "ƙaimi" daga gwamnatin Faransa don fara sabon zangon tattaunawa tsakanin ɓangarorin rikicin biyu.

Perriello ya ce Saudiyya da sha alwashin gabatar da taron sabuwar tattaunawa kuma Amurka na fatan za a ambata ranar da za a fara taron.

Tattaunawa mara tasiri

Tattaunawar da aka yi a baya a garin Jeddah na Saudiyya ta gaza samar da tabbatacciyar yarjejeniya.

Perriello ya ce, "Duk da akwai tarin alamu na cewa yaƙin yana ƙazanta a wasu wuraren, abin ya dagule sosai har ta kai wasu yankunan da ke maƙotaka abin ya fara shafar su. Ina ganin akwai bababr buƙatar yunƙurin diflomasiyya don kawo ƙarshen wannan yaƙi".

Ya ƙara da cewa, "Za mu gwada yin amfani da duka hanyoyin da muke iya bi".

AFP