An kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Sudan.
An kashe Manjo Janar Yasser Fadlallah Al-Khidr Al-Saim ne a ranar Litinin a Nyala, babban birnin yankin Kudancin Darfur, kamar yadda shugaban kasar gwamnatin rikon kwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya tabbatar.
A wata sanarwa, Al-Burhan ya bayyana kisan Al-Saim a matsayin “kisan gilla”, yana mai cewa lamarin “cin amanar kasa ne da cin amanar mutum.”
Wata majiyar soji da te nemi a boye sunanta ta shaida wa TRT Afrika cewa an harbe Al-Saim ne a cikin cibiyar soji ta Nyala.
“Al-Saim shi ne babban kwamandan rundunar sojin Sudan na farko da aka kashe tun bayan fara yakin basasar kasar," a cewar rundunar sojin ta (SAF) a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Tun 15 ga watan Afrilun 2023 rikici ya barke a Sudan, yayin da dakarun SAF da na rundunar sa kai ta (RSF) suka gwabza a kan iko da kasar gabanin mika mulki ga farar hula.
A kalla mutum 3,900 ne suka mutu a Sudan tun fara wannan yaki, sannan fiye da mutum miliyan hudu sun rasa muhallansu, a cewar alkaluman hukumomi.
Har yanzu an gaza cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.