Harsasai a kasa a wata fafatawa da aka gwabza tsakanin rundunar RSF da ta SAF a Khartoum. / Hoto: Reuters Archive

Rundunar sojin sa-kai na Rapid Support Forces (RSF) ta ce ta kashe sojoji 260 na rundunar sojin Sudan (SAF) a yayin da rikici ke kara kamari a kasar.

A wata sanarwa da ta fitar RSF ta ce ta kuma kwace wani yanki na sashen da ke kula da tankokin yaki na rundunar SAF a kudancin birnin Khartoum tare da kwace motocin soji.

“Dakarunmu sun yi wata gagarumar nasara a filin daga yau kusa da sashen tankoki na rundunar SAF a yankin Al Shagara (na Khartoum), tare da kwace makamai da dama da kashe dakarun rundunar 260, sannan mun kama daruruwansu," ta fada a ranar Litinin.

Sai dai rundunar SAF ta yi watsi da ikirarin, tana tabbatar da cewa dakarunta na musamman sun dakile harin da RSF ta kai a sashen da ke kula da tankokin yakin nata.

“Dakarunmu sun dakile harin da bai yi nasara ba da RSF ta kai. Wani sashe na musamman na SAF ya yi nasara a kan RSF sannan har yanzu yana bibiya da kuma duba yankin da sashen tankokin yakin yake," a wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafukan sada zumunta.

Ganau sun ce an gwabza mummunan fada a ranar Litinin tsakanin bangarorin biyu a kudancin Khartoum da Omdurman, inda aka kai hare-haren sama sosai da tayar da bama-bamai da hare-haren jirage marasa matuka.

RSF ta sha kai hare-hare kan sashen tankokin yaki da ke yankin Al Shagara, lamarin da ke tursasa wa mazauna yankunan Gabra da Al Sahaf da sauran wurare barin gidajensu.

Dubban mutane aka kashe tare da raba mutum miliyan hudu da muhallansu tun bayan fara yaki tsakanin RSF da SAF a ranar 15 ga watan Afrilu, musamman ma a Khartoum da JIhar Darfur.

AA