Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shiga fadarsa ta sarauta da tsakar daren Asabar awanni bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi takardar kama aiki a matsayin Sarki.
Wasu bidiyoyi da aka riƙa wallafawa a shafukan intanet sun nuna jerin gwanon motocin Sarkin tare da rakiyar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo yayin da suke shiga fadarsa yayin da suke shiga fadarsa da duhun dare.
Da alama batun shiga fadar ta Masarautar ya taso ne saɓanin yadda aka tsara tun da farko.
A lokacin da yake jawabi yayin miƙa takardar kama aiki ga Sarkin ranar Juma'a a fadar gwamnati, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Sarki Sanusi II zai zauna a masaukinsa inda za a ci gaba da al'amuran sarauta zuwa wani lokaci.
Sai dai wasu na ganin sauya wannan shawarar da shigar Sarki Sanusi II fadar Kano cikin dare ba za ta rasa nasaba da wasu abubuwa da suke tasowa ba.
Bayanai daga wasu majiyoyi na nuna cewa, Sarkin Kano wanda aka sauke Aminu Ado Bayero yana shirin komawa Kano da safiyar Asabar don shiga fadar ta Masarautar Kano a matsayin sarki.
Aminu Ado Bayero dai yana wata ziyarar aiki a Kudancin Nijeriya lokacin da gwamnan Kano ya sauke shi da sauran sarakunan jihar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduja ta naɗa.
Sai dai bayanai sun nuna cewa ya isa Kano da sanyin safiyar Asabar.
A ranar Alhamis ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da Ƙudurin Gyaran Dokar Masarautu ta Kano ta 2019, wacce ta ƙirƙiri masarautu biyar a Kano, sannan Gwamna Abba ya sa mata hannu.
Gwamnan ya bayyana ƙara cewa "saboda haka bisa canji da aka yi na wannan doka, a yau ni ma na yarda, majalisa ta yarda, an dawo da Mai Martaba Malam Sanusi Lamiɗo Aminu Sanusi wannan kujera ta Sarkin Kano."
"Kowa ya riga ya san cewa bisa waccan doka ta baya wadda suka rusa suka lalata, Sarki Malam Muhammadu Sanusi Aminu Sanusi shi ne Sarki a wancan lokaci," in ji gwamnan na Kano.
A ranar Alhamis ɗin ne dai ɗaya daga manyan Hakiman Masarautar Kano, Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar da ƙara kotu yana neman a hana gwamnati aiki da sabuwar Dokar Masarautun.
Takardar kotun, wacce aka ringa yaɗawa a kafofin sada zumunta na intanet, ta umarci duka waɗanda aka yi ƙara da su tsaya kada su ɗauki wani mataki har zuwa lokacin da kotun za ta saurari batun.
To sai dai a lokacin da yake jawabi bayan bai wa Sarki Sanusi II takarda a ranar Juma'a, Gwamna Abba Kabir ya ce umarnin da aka karɓo daga kotun ya makara.
“Na kafa hujja da cewa na sa hannu a kan Dokar Masarautar Kano da ƙarfe biyar na yamma, amma sai ƙarfe biyu na dare wani ya zo ya ce wai wannan abin bai yi ba,” a cewar gwamna Abba.
“Mun sa hannu da ƙarfe 5:20, wai alƙalin ma da ya ba da odar yana Amurka ya ba mu oda.”
Ya ƙara da cewa “Idan kuma akwai lauya da zai ce mana abin da muka yi ba daidai ba ne, mu ma muna da namu lauyan da zai ce daidai ne.”
“Abin da majalisa ta yi shi ne ƙwato wa wanda aka cuta haƙƙinsa,” a cewar Abba Kabir.
Gwamna Abba ya ce doka ce ta ba su damar gyaran dokar, kuma sun yi abin da ya kamata.
“Saboda haka doka ta zauna a jihar Kano daram dam,” in ji Gwamna Abba.
“Idan al’ummar jihar Kano suka karɓa, to kowa ma ya je inda zai je, don mu al’ummar jihar Kano ne suka zaɓe mu.”
Wasu bayanai dai na cewa an jibe jami'an tsaro da dama a ƙofar shiga Fadar Masarautar ta Kano ranar Juma'a da maraice.