Kusan watanni bakwai bayan soma yaki tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF, rikicin ya sa sama da rabin jama'ar kasar na bukatar agajin jinkai, wanda hakan ya sa ake fargabar za a iya sake shiga halin da aka shiga a lokacin yakin Darfur shekaru 20 da suka gabata.
"Abin da ke faruwa yana da nasaba da mummunar mugunta," in ji jami'ar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya a Afirka a ranar Juma'a.
Sudan ta shiga rudani tun bayan da aka soma yaki a tsakiyar Afrilun bana, a lokacin da aka soma takun saka wadda ta zama babban rikici tsakanin shugaban sojojin na Sudan Janar Abdel Fattah al- Burhan da kuma kwamandan rundunar Rapid Support Forces wato Janar Mohamed Hamdan Dagalo.
Sai dai Clementine Nkweta-Salami, wadda ita ce shugabar tsare-tsaren ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta shaida wa wani taron manema labarai na Majalisar Dinkin Duniya cewa "yanayin ya munana kuma yana da daga hankali" kuma "a gaskiya, muna da karancin kalmomi da za mu bayyana munin abin da ke faruwa." Ta jaddada cewa "Rikicin Sudan ya yi munin da irinsa kadan ne a duniya".
Ta ce ana ci gaba da gwabza fada duk da cewa bangarorin da ke gaba da juna sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya bayan tattaunawar zaman lafiya a Jeddah da ke kasar Saudiyya, inda suka yi alkawarin kare fararen hula tare da samar da agajin jin kai ba tare da tsangwama ba ga mutane miliyan 25 da ke bukatar taimako.
Janarorin da ba sa ga maciji da juna sun amince su kama wata gidauniyar jin kai, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, in ji Nkweta-Salami. Haka kuma bayan taron a ranar Litinin, Majalisar tana fatan janarorin su aiwatar da abubuwan da suka yi alkawari a Jeddah.
Ta bayyana cewa bangaren lafiya na kasar - wanda sama da kaso 70 cikin 100 na bangaren na wuraren da ake rikici ba su aiki - inda majalisar ta nuna damuwarta sakamakon barkewar cutar kwalara da maleriya da bakon dauro.
Abin da muka gani tana karuwa ita ce yunwa," in ji Nkweta-Salami, da kuma tsantsan rashin abinci ga yara.
Majalisar Dinkin Duniya na son tallafa wa kusan mutum miliyan 12 - wato kusan rabin wadanda suke neman agaji. Sai dai bukatar da majalisar ke da ita na kusan sama da dala biliyan 2.6 na agajin jinkai a Sudan a 2023 kusan kaso daya bisa uku ne kawai aka samu, inda Nkweta-Salami ta bukaci aka kara samar da karin kudi.