Shugabannin kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar kulla kawancen tsaro da tattalin arziki a tsakaninsu.
Sun kulla yarjejeniyar ce ranar Asabar a Bamako babban birnin Mali.
"A yau, ni da shugabannin kasashen Burkina Faso da Nijar, mun sanya hannu kan yarjejeniyar Liptako-Gourma da ta kafa Kawancen Kasashen Sahel, wato Alliance of Sahel States (AES), wanda zai tattaro bayanai kan sha’anin tsaro da taimaka wa dukkan al’ummominmu", in ji shugaban kasar Mali, Assimi Goita, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter.
Yankin Liptako-Gourma – inda kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suka yi iyaka da juna – ya dade yana fama da matsalolin hare-haren masu tayar da kayar baya.
Kasashen uku suna fuskantar gagarumin rashin tsaro wanda ya somo daga Mali a 2012 sannan ya watsu zuwa Nijar da Burkina Faso a 2015.
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tiani ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai cike da ''tarihi'' yana mai cewa "dukkanmu za mu gina al’ummar yankin Sahel mai cike da zaman lafiya da tsaro da hadin kai.''
Dukkan kasashen uku sun yi fama da juyin mulki tun shekarar 2020, na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a Jamhuriyar Nijar a watan Yulin da ya gabata inda sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Kasashen sun kafa kungiyar kawance ta Alliance of Sahel States ce a yayin da dukkansu suke rigima da ECOWAS sakamakon juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Labari mai alaka: Mali da Burkina Faso sun tura jiragen yaki Nijar
ECOWAS ta yi barazanar yin amfani da karfin soji domin dawo da Bazoum kan mulki amma kasashen uku sun ce za su mayar da martani.
"Wannan kawancen zai kasance na soji da tattalin arziki tsakanin kasashen uku", a cewar Ministan Tsaron Mali Abdoulaye Diop a yayin taron manema labarai ranar Asabar.
Ya kara da cewa "babban burinmu shi ne yaki da ta'addanci a kasashen uku".
Baya ga fama da kungiyoyin ta'addanci da ke da alaka sa Al Qaeda da Islamic State, Mali tana kuma gwagwarmaya da masu tayar da kayar baya na kungiyoyin makiyaya.