Gwamnatin Nijeriya ta yi kari ga kudin makarantun sakandire na tarayya wadanda aka fi sani da Unity Schools a fadin kasar daga naira 45,000 zuwa naira 100,000.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin babbar daraktar sashen makarantun sakandire na ma’aikatar ilimi ta Nijeriya Hajiya Binta Abdulkadir, ta yi karin bayani kan karin kudin makarantar.
Kudin makarantar zai soma aiki daga zangon karatun farko na wannan shekara.
Ga dai yadda karin zai shafi dalibai: Kudin koyarwa: Kyauta
Kudin dakunan kwanan dalibai: N30,000 (Ga masu kwana)
Kudin uniform: N25,000 (Daga Jss1 zuwa SS1)
Kudin littafan karatu: N15,000
Kudin littafan rubutu: N5,000 (sau daya a shekara)
Takardun Propectus: N1,000
Kudin taka-tsan-tsan: N,1000 (sau daya a shekara)
I.D Card: N1,000
Kayan rubutu: N1,000
Kudin kulob da kungiyoyi: N1,000
Wasanni: N1,000
Kiwon lafiya: N2,000
Koyon sana’a: N1,000
Kayan aiki: N2,000
Tsaro: N1,000
Internet/duba sakamako: N3,000
Skool Media: N3,000
Karin darasi: N2,000
Inshora: N5,000
Jimlar jerin wadannan abubuwan sun zama naira N1,00,000.
Ko a kwanakin baya sai dai wasu jami'o'i a kasar suka sanar da karin kudin makaranta, inda wasu jami'o'in suka yi kari fiye da kashi 100.