Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce ta fara gudanar da bincike dangane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi kan cewa fararen hula da ‘yan bijilanti sun rasu yayin wani samame da ta kai a Jihar Zamfara.
A ranar Lahadi ne dai kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito cewa wani hari ta sama da sojojin ƙasar suka kai ya kashe farar hula 16 ciki har da ‘yan sa-kai bisa kuskure a ƙauyen Tungar Kara na jihar Zamfara.
Harin na sama, wanda aka ƙaddamar don fatattakar ɓarayin daji a yankin, ya shafi dakarun sa-kai na jihar Zamfara (ZCPG) da ‘yan bijilanti da kuma sauran mutanen gari waɗanda suka haɗu domin kare mutane daga ‘yan bindiga.
Sai dai a sanarwar da ta fitar a ranar, Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta bayyana cewa ta samu ƙorafe-ƙorafe masu “ƙarfi” game da rasa rayukan ‘yan bijilanti da farar hula a yayin samamen da ta kai Tungar Kara.
Mai magana da yawun sojin saman ƙasar Olusola F Akinboyewa ya bayyana cewa sojin saman ƙasar sun san darajar ran duk wani ɗan Nijeriya.
“Don haka, ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike, domin tabbatar da sahihancin rahotannin, inda za a sanar da sakamakonsu yadda ya kamata domin faɗakar da jama’a.”
A wata sanarwa da ta fito daga gidan gwamnatin Zamfara da ke Gusau, Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana alhininsa ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
'An ɗauka ‘yan bindiga ne'
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauka waɗanda lamarin ya rutsa da su ‘yan bindiga ne da suke tserewa daga Gidan Makera da ke garin Boko na Ƙaramar Hukumar Zurmi.
“Mun samu rahotanni daban-daban na harin sama da ɓangaren sojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma ya ƙaddamar a ƙarshen mako a yankin Ƙaramar Hukumar Maradun da Zurmi," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
"Sai dai kuma, harin ya rutsa da wasu ‘yan sa-kai ɗin da kuma sauran ‘yan bijilanti a lokacin harin Tungar Kara, lamarin da ya haddasa rasa rayuka."
Aukuwar lamarin a baya
Wannan ifital’in ya daɗa bayyana irin ƙalubale da kuma hatsarin da ke tattare da yaƙar ta’addanci a yankin arewacin Nijeriya inda iya bambancewa ko akasin haka tsakanin mayaƙa da farar-hula ka iya janyo rasa rayuka.
Maharazu Salisu Gado Faru, wani ɗan majalisa da ke wakiltar mazaɓar Maradun II a majalisar dokokin jihar Zamfara, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce harin na sama ya afka wa ‘yan sa-kai da suka shirya domin tinkarar ɓarayin daji ne.
Iftila’in na jihar Zamfara ya biyo bayan wani harin da aka kai kan farar-hula bisa kuskure a watan Disamban shekarar 2023 a lokacin da harin sojin Nijeriya ya afka wa wani taron maulidi a ƙauyen Tudun Biri na jihar Kaduna inda aka kashe mutum 85.
Kazalika a watan Janairun shekarar 2017, aƙalla mutum 112 ne aka kashe a lokacin da jirgin yaƙi ya kai hari a wani sansani inda ‘yan gudun hijira 40,000 daga garin Rann suke kusa da kan iyakar ƙasar da Kamaru.
Waɗannan kurakuran sun nuna ƙalubalen da ake fuskanta a Nijeriya a yaƙi da ta’addanci inda farar-hula suke shiga hatsari a lokacin musayar wuta.