Wau mata da suka rasa muhallansu sun samu mafaka a yankin Port Sudan da ke Sudan, ranar 29 ga watan Agusta, 2024. / Hoto: Reuters Archive

Majalisar Ɗinkin Duniya ta wallafa wani rahoto mai tayar da hankali ranar Talata wanda ya nuna yadda mata da 'yan mata suke fuskantar bala'i sakamakon yaƙin da ke faruwa a Sudan, ciki har da wata mace da ta ce an umarci ta kashe kanta da wuƙa maimakon ta mutu sanadiyar fyaɗe.

A yayin da yaƙi yake ci gaba da ƙarami a ƙasar, an kashe fararen-hula aƙalla 124 a jihar Al Jazirah da ke tsakiyar Sudan tun daga ranar 20 ga watan Oktoba, sannan mutum fiye da 135,000 sun tsere zuwa wasu jihohi, a cewar Asusun Kula da Ƙidayar Jama'a na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya ƙware wajen kula da lafiyar mata da yara.

Ya ƙara da cewa cikin mutanen da suka tsere har da mata masu ciki 3,200.

Rikici ya ɓarke a Sudan ne a watan Afrilun 2023 tsakanin shugaban rundunar sojojin ƙasar, Abdel Fattah al Burhan, da shugaban rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces, kuma tsohon mataimakinsa, Mohamed Hamdan Dagalo.

Yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba fiye da mutum miliyan 11 da muhallansu, a cewar Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Asusun Kula da Ƙidayar Jama'a na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ambato ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Al Jazirah tana cewa bincikenta ya gano cewa an yi wa mata 27 fyaɗe waɗanda shekarunsu suka kama daga shida zuwa 60.

"Waɗannan alƙaluma kaɗan ne daga cikin lalata da ake yi da mata wadda ta zama ruwan-dare a yanzu haka," in ji Asusun.

Asusun ya ambato wata mata mai suna Maria, mahaifiyar 'ya'ya biyu, tana cewa wasu 'yan bindiga sun "ci zarafinmu, sun dake mu, sannan suka sanya mana bakin bindiga kana suka binciki 'ya'yanmu mata."

Kazalika Asusun ya ambato wata yarinya da bai ambaci sunanta ba da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira tana cewa an ba ta zaɓin da ya ɗaga mata hankali.

"Maza, waɗanda suka haɗa da yan'uwanmu da iyayenmu da kawunanmu, sun ba mu wuƙake sannan suka ba mu umarnin kashe kanmu muddin 'yan bindiga suka yi barazanar yi mana fyaɗe," in ji ta.

AFP