Hukumomin Nijeriya sun ce 'yan kasar sun makale a kan iyakar Masar a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin da jirgin sama zai kwashe don kai su Abuja, babban birnin kasar.
Ranar Alhamis ne aka soma kwaso kashin farko na dalibai 1600 daga Sudan bayan sun kwashe kwanaki suna korafi game da mawuyacin halin da suka shiga sakamakon rikicin da ya barke a kasar tsakanin sojoji da dakarun runduna ta musamman ta Rapid Response Force, RSF.
Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya, NEMA ta bayyana cewa tana sa rai daliban za su isa Abuja ranar Juma'a idan jirgin saman Air Peace ya kwaso su daga yankin Aswan na kasar Masar bayan sun isa can daga Khartoum.
Sai dai a wani sakon Twitter da hukumar da ke kula da 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje ta wallafa ranar Alhamis da tsakar dare, ta ce 'yan kasashen waje kusan 7000, ciki har da 'yan Nijeriya sun makale a Masar.
Sakon ya ambato shugabar hukumar, Abike Dabiri, tana cewa "an hana fiye da mutum 7000 'yan kasashe daban-daban, ciki har da 'yan Nijeriya damar tsallakawa kan iyaka don shiga Masar" tun da suka isa can ranar Alhamis da maraice.
Ta yi kira ga hukumomin Masar su bar mutanen su wuce don isa wuraren da jirage za su kwashe su don kai su kasashensu.
Abike Dabiri ta kara da cewa ofishin jakadancin Nijeriya da ke kasar yana aiki tukuru don shawo kan matsalar "a yayin da hukumomin Masar suka dage cewa sai kowanne dan Afirka ya samu biza kafin a bar shi ya tafi kasarsa."
Tsaka-mai-wuya
Tun da farko daliban Nijeriya sun rika korafi game da mawuyacin halin da suka shiga a Sudan tun da aka soma rikicin inda suka yi zargin cewa hukumomi sun ki kwaso su zuwa gida.
Daga bisani gwamnatin kasar ta hannun hukumar NEMA ta bayyana cewa ta samar da motocin bas-bas guda arba'in domin kwaso daliban.
“Tawagar motoci 13 da ke dauke da kashin farko na wadanda aka kwaso daga Khartoum na kasar Sudan tana tafiya zuwa yankin Aswan na kasar Masar kuma daga nan jirgi zai dauke su zuwa Nijeriya,” in ji NEMA.
Sai dai daga bisani daliban sun wallafa bidiyoyi a soshiyal midiya inda suka rika korafi kan yadda motocin da suka debo su suka lalace a dokar-daji.
Amma daga baya hukumomi sun motocin sun ci gaba da tafiya a kan hanyarsu ta isa Masar.
A gefe guda, ma'aikatar wajen Nijeriya ta ce za ta soma kwashe kashi na biyu na 'yan kasar daga Sudan a yau Asabar.
Ta yi kira ga wadanda ke son komawa Nijeriya su hadu a Jam'iar Al-Razi da kuma International University of Africa da safiyar nan don a kwashe su.