Shugaban Rasha Vladimir Putin ya taba yin kira da a samar da hanyoyin hana yaduwar makamai masu guba a duniya. / Hoto: AA

Rasha ta zargi Amurka da mayar da wani bangaren aikinta ''wanda ba a kammala shi ba'' na Ukraine kan binciken makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka.

Ana kan gudanar da wannan aiki a kasashen Nijeriya da Kamaru da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Saliyo da kuma Uganda, a cewar Igor Kirillov, shugaban sojin Rasha da ke kula da ayyukan binciken sinadarai da kare halittu, a yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Moscow a ranar Talata.

"A yau, idan muka yi misali da Nijeriya, za mu ga cewa manufofin da aka bayyana na ayyukan da ake son aiwatarwa wajen inganta kiwon lafiyar al'umma ba su yi daidai da abin da yake a zahiri ba," in ji shi.

Jami’in na Rasha ya kara da cewa ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi ikirarin cewa ayyukan nazarin halittu a Nijeriya sun mayar da hankali a yaki da cutar kanjamau ta HIV/AIDS, kuma kashi 60 cikin 100 na masu fama da cutar a kasar, sun bi tsarin da aka ware na karbar maganin rage yaduwar cutar.

"Adadin masu cutar HIV bai sauya sosai ba a kasar, a halin da ake ciki yawan mutanen da ke dauke da cutar kusan daidai yake da na shekarar 2009, kazalika yawan mace-mace da ake samu a tsakanin masu dauke da cutar ya ragu," in ji Kirillov.

Jami'in ya nuna shakku kan manufar boye shaidun da za su iya bankado babban dan kwangilar Pentagon, kamar yadda bayanan cikin takardun kwagilar suka nuna.

"Takardu sun jaddada bukatar a takaita bincike a kan dan kwangilar, wato ( kwararrun Pentagon) kan su gudanar da gajerun tafiye-tafiye zuwa kasar Afghanistan da Iraki daga ofishinsu da ke birni Dubai idan har bukatar hakan ta taso," in ji shi.

Kirillov ya kara da cewa, "don kauce wa duk wasu zarge-zarge kan ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, sai aka aiwatar da ayyukan karkashin ma'aikatar harkokin wajen Amurka."

TRT Afrika