Cututtukan Ebola da Korona ne dai suka fi kaurin suna a nahiyar wadanda aka yi zaton za su kusan karar da jama'ar nahiyar. Photo/AA

Daga Mustapha Musa Kaita

A ranar 7 ga watan Afrilun kowace shekara ce Hukumar Lafiya ta Duniya ta ware a matsayin ranar Lafiya ta duniya.

A bana, wannan ne karo na 75 da ake bikin wannan rana. A 1948 ne kasashe da ke fadin duniya suka hadu domin kafa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO domin bai wa duniya kariya ta yadda mutane za su zauna cikin aminci da samun kulawa ta fannin lafiya mafi inganci.

Nahiyar Afrika dai ta sha fama da cututtuka da dama inda kuma ta shawo kansu.

Masana na ganin sakamakon karancin kayayyakin aiki ta bangaren kiwon lafiya, shi ya sa wasu cututtukan suke kara ta’azzara da kuma daukar rayuwakan mutane.

Albarkacin wannan rana ta lafiya ta duniya, mun yi duba dangane da irin cututtukan da nahiyar Afrika ta yi fama da su da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da su nan gaba.

Ebola

A shekarar 2014 ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da rahoton barkewar cutar Ebola a kasar Guinea da ke Yammacin Afrika.

Masana dai sun ce cutar ta samo asali ne daga tsuntsaye irin su jemage. Cutar ta soma yaduwa zuwa kasashen da ke makwaftaka da Guinea kamar Saliyo da kuma Liberia.

Alamomin cutar na farawa ne kamar cutar Malaria da zazzabin typhoid ko kuma sankarau wanda hakan ke sawa a yi wahala wurin gano abin da ke damun mutum.

Wanda ya kamu da cutar kan nuna alamomi kamar zazzabi da gajiya da ciwon jiki da gabobi da ciwon kai da mashako da amai da gudawa.

Haka kuma ana samun kuraje a jiki da kuma zubar da jini ta cikin jiki.

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta bayyana cewa bayan an shawo kan barkewar wannan cuta tsakanin 2014 zuwa 2016, an tabbatar da mutum 28,610 ne suka kamu da cutar sai kuma mutum 11,308 suka mutu sakamakon cutar.

Sai dai har yanzu ana samun bullar cutar jefi-jefi musamman a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Masana na bayar da shawarar kiyaye cutar musamman a yankunan da ta fi bulla ta hanyar guje wa cin wasu namun daji da suka hada da jemage da birai.

Kwalara

Cutar kwalara na sanadin mutuwar dubban yara a fadin duniya. Photo/Getty Images

Cutar kwalara ko kuma amai da gudawa cuta ce da take iya kashe mutum cikin sa’o’i bayan kamuwa da ita.

Har yanzu kwalara babbar barazana ce ga lafiya al’umma, inda ake samun mutum miliyan 1.3 zuwa miliyan hudu da ke kamuwa da cutar a duk shekara, kamar yadda hukumar CDC ta bayyana.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa ana samun tsakanin mutum 21,000 zuwa 143,000 da ke mutuwa sakamakon wannan cuta a duk shekara.

A 2018, an samu barkewar kwalara a Kamaru inda mutum 237 suka kamu da cutar sannan 17 suka rasa rayukansu.

Haka kuma a Habasha a 2019, mutum 525 aka tabbatar sun kamu da cutar sa’annan 16 suka rasu, kamar yadda CDC ta bayyana.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana tsafta a matsayin wani ginshiki na yaki da cutar kwalara.

Ta ce akwai bukatar a sha ruwa mai tsafta da kuma cin abinci mai tsafta.

Haka kuma ta ce akwai bukatar a rinka wanke hannu da sabulu idan an yi bayan gida a duk lokacin da mutum zai ci wani abinci.

Zazzabin Lassa

An gano cutar Lassa a Nijeriya a karon farko a 1969 Photo/ AA

An soma gano wannan cuta ne a Nijeriya kuma an rada mata sunan ne bayan garin da aka fara gano ta.

Masana dai sun yi itifakin dabbobi irin su bera ne ke jawo wannan cuta.

Hukumar CDC ta bayyana cewa adadin wadanda ke kamuwa da wannan cuta a Yammacin Afirka a duk shekara ya kai mutum 100,000 zuwa 300,000 haka kuma akwai akalla mutum 5,000 da cutar ke kashewa.

Sai dai hukumar ta ce babu tabbaci kan wannan adadin sakamakon ba a sa ido yadda ya kamata kan cutar.

Hukumar ta CDC ta ce akasari alamomin cutar suna farawa ne a hankali. Suna farawa ne da gajiya sai ciwon kai da na makogwaro da ciwon kirji da amai da da gudawa.

Kasashen Afirka sun sha fama da bullar wannan cuta amma suna samun nasarar dakile ta.

Kasashen da cutar ta fi addaba sun hada da Nijeriya da Liberia da Jamhuriyyar Benin.

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Amurka ta bayyana cewa hanya ta farko ta kare kai daga kamuwa da wannan cuta ita ce mutum ya guje wa mu’amula da beraye, musamman ma a yankunan da ake samun wannan cutar.

Hukumar ta ce akwai bukatar a rinka saka abinci a cikin kwanuka wadanda beraye ba su iya fasawa haka kumata ce akwai bukatar a rinka barin gida cikin tsafta a kullum domin guje wa beraye.

Haka kuma hukumar ta ce masu cin beraye na cikin hatsarin kamuwa da wannan cuta inda ta ce a guji cin duk wani nau’i na bera.

Cutar Korona

Cutar numfashi ta korona wadda aka fi sani da Covid-19 dai ta faro ne a karshen shekarar 2019 a garin Wuhan da ke China.

Daga nan ne ta yi ta yaduwa zuwa kasashen duniya har ta game duniya baki daya ta zama annoba.

Zuwa Fabrairun 2023, sama da mutum 12,216,748 ne aka tabbatar sun kamu da cutar ta korona sa’annan 256,542 suka rasa rayukansu sakamakon cutar, kamar yadda hukumar CDC ta bayyana.

A lokacin da cutar korona ta bulla, an yi hasashen cewa za ta yi barna a Afirka inda aka yi zaton cewa miliyoyin mutane za su rasa ransu, amma bayanai sun nuna hasashen bai zama gaskiya ba.

Zai yi wahala dai a gano takamaiman adadin mutanen da suka kamu ko kuma suka mutu sakamakon cutar korona a Afirka sakamakon karancin kayan aiki da kimiyya da gwajin cutar.

Sauran cututtuka da Afirka ta sha fama da su

  • Cutar Marburg
  • Diphtheria
  • Kyanda
  • Farankama.

TRT Afrika