Gwamnan Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya yi umarni a gudanar da bincike kan mutanen da gwamnatinsa ta bai wa kwangilar raba wa al'ummar jihar abinci a watan azumi.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan ya kai ziyarar ba-zata a ɗaya daga cikin cibiyoyin da aka ɗora wa alhakin raba abincin azumi da ke ƙaramar hukumar Birni domin gane wa idanunsa abin da ke faruwa.
Sai dai ya bayyana matuƙar ɓacin ransa dangane da ingancin abincin da ake bai wa jama'a yana mai cewa ba zai lamunci hakan ba.
A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ranar Juma'a da maraice, an ga gwamnan na Kano a cibiyar raba abincin inda ya ɗauki fanken da ake rabawa yana cewa "ku kalli wannan shirmen". Ya tambayi matan da ke soya fanken wanda ya sa su aikin inda suka bayyana cewa wani jami'in gwamnati ne.
Daga nan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tambaye su ko ana zuwa ana duba yadda suke gudanar da aikinsu. Matan sun bayyana cewa wasu jami'a suna zuwa.
Gwamnan ya umarce su da su inganta yadda suke soya fanken, yana mai cewa "kada na sake dawowa na tarar an yi abin da ba daidai ba."
Daga bisani Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa saƙo a shafukansa na sada zumunta cewa ya bayar da umarni a gudanar da bincike kan yadda ake raba abincin na azumi.
"Da maraicen yau, na kai ziyara Gidan Maza, ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke rabon abincin azumin Ramadan a ƙaramar hukumar Birni. Abin da na gani a wannan ziyara ta ba-zata yana da takaici, duk kuwa da isasshen abinci da muka bai wa cibiyar. Na yi umarni a gudanar da cikakken bincike, kuma na bayar da umarni a yi gaggawar sauya tsarin wannan shiri," in ji gwamnan Kano.