Daga Mustapha Musa Kaita
Jama’a da dama musamman mazauna Abuja sun shiga fargaba tun bayan da Ezenwo Nyesom Wike ya zama sabon Ministan Babban Birnin Nijeriya, Abuja.
Wike ya yi fice a Nijeriya sakamakon irin yadda yake gudanar da siyasarsa tun a baya ganin cewa ba ya tsoron ya fadi ra’ayinsa.
Maradinsa ba ya kunya, jim kadan bayan rantsar da shi sai kuwa ga Wike ya fara ba da sanarwa masu zafi har biyu.
Na farko dai ya gargadi masu gine-gine ba bisa tsarin birnin taryya ba cewa za a iya rusa gidajensu, na biyu kuma ya ce ba zai yarda a dinga kiwon shanu barkatai a kan titunan Abuja ba.
Dama ita Abuja a bisa yadda aka gina ta, ta zo ne da tsare-tsaren yadda komai zai kasance a muhallinsa, amma masu sharhi na cewa a yanzu abubuwa suna lalacewa ta wannan fanni, sannan ana ganin yadda kiwaon shanu a cikin birnin ya zama abin yi sosai.
Nyesom Wike ya yi suna ko kuma a ce ya soma fice ne a lokacin da ya zama Karamin Ministan Ilimi a Nijeriya a 2011.
Bayan haka a 2012 Shugaba Goodluck Jonathan ya ba shi mukamin babban minista na riko a ma’aikatar ta ilimi.
A halin yanzu da ya zama sabon Minsitan Abuja, masana siyasa irin su Dakta Faruk BB Faruk wanda malamin koyar da siyasar tattalin arziki ne a Jami’ar Abuja, ya shaida wa TRT Afrika cewa da alama idan Wike ya soma aiki a Abuja dole ne kowa ya ji motsin shi.
“Shi dama yana nuna tsohuwar katafila ce, wadda ga aiki amma ga shan mai da tumbudo hayaki da yawa da kuma saurin daukar zafi, saboda haka tabbas idan Wike ya soma aikinsa kowa zai ji karar motsin shi.
Ko tsarin gudanar da mulkin Wike na bayar da sakamako mai kyau?
Dakta BB Faruk ya bayyana cewa tabbas za a ga ayyuka musamman kananan ayyukan da za su shiga har cikin gidajen mutane da unguwanni.
Haka kuma ya bayyana cewa Wike zai kara matsa kaimi wurin karbar haraji wanda a cewarsa lamari ne wanda aka yi sakaci a baya.
“Katafila mai son aiki amma ba burki ba ribas ba iya kwana, za a tafi a cimma bukatun da ko don su aka shirya ko ba don su aka shirya ba za su tabbata,” in ji Dakta Faruk.
Ya bayyana cewa a halin yanzu abubuwan da mutanen Abuja suke so su ne tsaro da wutar lantarki da ruwan sha, duk su inganta inda a cewarsa, kuma duk Wike zai iya tabbatar da hakan.
“Zai kada gangar wadannan ayyuka kuma za a zo a yi rawar yin wadannan ayyukan saboda Allah Ya ba shi kuzarin nuna wannan matsayi na aiki.
“Idan ka kalli Jihar Ribas, za ka ce da irin wannan tafiya ya nuna bajintar za a iya taba wasu abubuwa su yiwu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa irin wannan bajintar Mista Wike ya nuna a Jihar Ribas ya yi ayyuka
Karfin siyasar Wike
Nyesom Wike ya soma fice a Jihar Ribas a lokacin da ya yi shugabancin Karamar Hukumar Obio Akpor tun daga 1999 har zuwa 2007.
Lokacin da siyasar Wike ta kara karfi a Nijeriya shi ne lokacin da ya zama Gwamnan Jihar Ribas, wadda jiha ce mai dumbin arzikin man fetur a Nijeriya.
Jihar Ribas ta kasance jiha daya a Nijeriya mai matatun mai biyu.
Nyesom Wike ya shafe shekaru takwas a kan mulki a matsayinsa na gwamna a Ribas, wanda ya kasance mutum mai sa mutane raha da nishadi sakamakon yadda yake taka rawa a duk lokacin da aka saka kida musamman a wuraren taro.
Daya daga cikin nasarar da Wike ya samu a jihar ita ce aiwatar da shirin ilimi kyauta a makarantun firamare da sakandire na gwamnatin jihar.
Haka kuma Mista Wike din a 2019, ya sanar da biyan kudin jarrabawar JAMB kyauta ga daliban makarantun gwamnati a jihar.