Shugaban Hukumar Kula da Da'ar Ma'aikata ta Nijeriya Farfesa Isah Mohammed ne ya kai wa shugaban kasar fom din a fadarsa /Hoto: Presidency

Hukumar Kula da Da'ar Ma'aikata ta Nijeriya ta kai wa Shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado fom din bayyana kadarorinsa.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin soshiyal midiya Bashir Ahmed ne ya wallafa hotunan ziyarar da jami'an hukumar suka kai wa Shugaba Buharin a ranar Juma'a, kwana biyu kafin kammala wa'adin mulkinsa.

Shugaban Hukumar Kula da Da'ar Ma'aikata ta Nijeriya Farfesa Isah Mohammed ne ya mika wa shugaban kasar fom din a fadarsa ta Aso Rock.

Dama bisa ka'ida, hukumar kan bai wa masu mulki fom din su cike a lokacin da za su fara shugabanci, inda za su bayyana yawan kadarori da dukiyar da suka mallaka.

Kazalika ana sake umartar su da su cike fom din bayyana kadarorin a yayin da suke barin mulki.

Dokar kasa ce ta tanadi wannan tsari don a gane ko masu mulki sun yi sama da fadi da kudin al'umma a lokacin da suke kan shugabanci, ta hanyar la'akari da abin da suka mallaka kafin su hau, da kuma wanda suka mallaka a lokacin saukar su.

Abubuwan da Buhari ya mallaka a 2015

A watan Satumban 2015 watanni kadan bayan rantsar da shi, Shugaba Buhari ya bayyana kadarorin da ya mallaka kamar yadda sanawar Hukumar Kula da Da'ar Ma'aikata ta fada a lokacin.

Kadarorin sun hada da:

  • Hannun jari a kamfanin Berger Paints da Bankin Union da ba a fadi yawan adadinsu ba
  • Gidaje biyu ginin laka a mahaifarsa ta Daura
  • Filaye biyu; daya a Kano daya a Fatakwal
  • Ya mallaki motoci amma ba a fadi adadinsu ba. Biyu daga ciki shi ya saya da kudaden ajiyarsa, sauran kuma gwamnatin tarayya ce ta ba su a matsayin tsohon shugaban kasa
  • Sai kuma motocin da ya samu kyauta sakamakon lalata masa motarsa kirar Jeep a harin da Boko Haram suka kai wa ayarinsa a watan Yulin 2014 a Kaduna
  • Gona da shanu 270 da tumaki 25 dawakai biyar da tsuntsaye.

TRT Afrika da abokan hulda