Ana sa ran kammala tantancewar a ranar Alhamis 5 ga watan Yuni./ Hoto/NPP

Kwamitin da ke tantance ‘yan takara na Jam’iyyar NPP mai mulki a Ghana ya sanar da cewa zai soma tantance masu neman takarar shugabancin kasar daga Litinin 3 ga watan Yulin 2023.

Sakataren kwamitin Mista Evans Nimako ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito cewa 10 daga cikin 11 na masu neman takarar wadanda suka sayi fom domin sun cike shi domin shiga takarar gadan-gadan.

Masu neman takarar, wadanda ake sa ran za su hallara a gaban kwamitin a ranar 3 ga watan Yuli, sun hada da tsohon Ministan Cinikayya da Masana’antu, Alan Kwadwo Kyeremanten, da Mataimakin Shugaban Kasa, Dakta Mahamudu Bawumia da Kwadwo Poku wani masani kan makamashi.

Tsohon Ministan Makamashi, Boakye Kyeremanteng Agyarko da tsohon Sakatare Janar na Jam’iyyar NPP Kwabena Agyei Agyepong da dan majalisa mai wakiltar Tsakiyar Assin, Kennedy Ohene Agyapong duka a ranar Talata 4 ga watan Yuli za su hallara a gaban kwamitin.

Sai kuma a ranar Laraba 5 ga watan na Yuli wadanda za a tantance sun hada da Dakta Kofi Konadu Apraku da masanin tattalin arziki kuma tsohon Ministan Aikin Gona Dakta Owusu Afriyie da kuma dan majalisa mai wakiltar Essikado-Ketan, Joe Ghartey.

Sai kuma a ranar Alhamis za a karkare tantancewar da tsohon dan majalisar Mampong, Francis Addai-Nimako.

TRT Afrika