Nijeriya na ƙara adadin kuɗin da take kashewa kan tsaro a 'yan shekarun nan a daidai lokacin da take fama da matsalolin tsaro. / Hoto: NAF

Majalisar Zartarwar ta Tarayya ta amince da karɓo bashin kusan dala miliyan 618 domin sayen jiragen yaƙi na ƙasar Italiya ƙirar M-346 da kuma wasu makamai ga rundunar sojin saman ƙasar, kamar yadda ministan watsa labarai na ƙasar Mohammed Idris ya sanar a ranar Laraba.

A farkon watan nan, rundunar sojin saman ƙasar ta sanar da cewa za ta sayi jiragen yaƙi 24 ƙirar M-346 da kuma jirgi mai saukar ungulu 10 ƙirar AW109 a shirin rundunar na sabunta jiragen yaƙinta.

Ana sa ran kai jiragen uku na farko ƙirar M-346 a farkon shekarar 2025 sai kuma sauran da suka rage a kai su ƙasar a tsakiyar shekarar 2026, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana.

Nijeriya na ƙara adadin kuɗin da take kashewa kan tsaro a 'yan shekarun nan a daidai lokacin da take fama da matsalolin tsaro waɗanda suka haɗa da 'yan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar da kuma yaƙi da 'yan Boko Haram wanda aka shafe shekara aƙalla 15 ana gwabzawa a arewa maso gabas.

TRT Afrika