Hukumar Samar da Ruwa ta Legas ta yi gargaɗi kan shan ruwan da ba a tabbatar da tsaftar shi ba. / Hoto: Reuters

Hukumomin Lafiya a Nijeriya na gargaɗi dangane da ɓarkewar cutar kwalara da ta kashe aƙalla mutum 30 a bana, akasarinsu a Legas.

Kwalara cuta ce wadda ke kama hanji wadda ke bazuwa ta hanyar gurɓataccen abinci ko ruwan sha. Tana jawo gudawa da amai da murɗawar ciki – a wani lokacin har ta yi kisa.

A wata sanarwa da Gwamnatin Legas ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa mutum 15 suka rasu zuwa yanzu a jihar inda 350 kuma aka tabbatar da sun kamu da cutar.

Hukumar Samar da Ruwa ta Legas ta yi gargaɗi kan shan ruwan da ba a tabbatar da tsaftar shi ba.

“Kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Legas ta bayyana, ana alaƙanta babban dalilin da ke jawo da shan gurɓataccen ruwa da rashin tsaftar muhalli,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata, Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa NCDC ta gargaɗi ‘yan ƙasar dangane da ƙaruwar cutar a daidai lokacin da damuna ke ƙara kankama a ƙasar.

Hukumar ta ce aƙalla mutum 30 suka rasu tun daga farkon wannan shekarar. Wata ɓarkewar cutar da aka samu a bara ta kashe aƙalla mutum 128 sannan aka gano mutum 3,600 waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a faɗin Afirka idan aka kwatanta da shekarar 2022 wadda aka samu mutuwar mutum biyu.

Nijeriya musamman na fama da barazanar ɓarkewar kwalara. A 2021, cutar ta kashe sama da mutum 2,300, musamman yara da ke ƙasa da shekara 14 kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar.

AFP