Daga Charles Mgbolu
A kalla manyan rukunin shaguna 17 aka rushe a wata babbar kasuwar da ke Jihar Legas a Nijeriya.
Hukumar kula da gine-gine ta jihar ta ce an rushe gine-ginen ne saboda ba a yi su yadda ya kamata ba kuma suna saka rayuwar mazauna wajen a cikin hadari.
Mafi yawan shagunan da ke Kasuwar Alaba da ke yankin Ojo na sayar da kayan lantarki ne.
Mabambantan ra'ayoyi
A wata sanarwa da babban manajan hukumar kula da gine-ginen Gbolahan Oki ya fitar, ya ce tun a shekarar 2016 ya kamata a rushe wasu daga cikin gine-ginen.
An tura tawagar 'yan sanda don su saka ido a wajen lokacin da katafila ke rusa gine-ginen, yayin da mutane kuma suke kallo daga can nesa.
'Yan kasuwar da ke harkoki a wajen sun bayyana mabambanta ra'ayoyi a hirarsu da TRT Afrika.
Drogba Azoson, wani da yake da rumfa a kasuwar ya ce rusau din ya yi daidai don kare bala'in rasa rayuka da za a iya samu nan gaba.
"Abin bai shafi shagona da ke daya daga cikin rukunin shagunan ba. Yawancin gine-ginen da aka rusa din suna daf da rushewa ne wasu kuma suna kan magudanar ruwa," in ji Azoson.
Shi kuma wani dan kasuwar da ya zanta da TRT Afrika da ya bukaci a boye sunansa, ya ce ba a sanar da shi komai a kan batun rusau din ba.
"Ba a sanar da ni komai ba don na shiryawa hakan. Na biya kudin hayata na shekara biyu. Yanzu da aka rushe ginin wa zai biya ni kudina? in ji mutumin.
Tuntuni ya kamata a rusa gine-ginen
Gwamnatin Nijeriya ta ce 'yan kasuwar sun dade suna kawo tarnaki wajen rusau din, "ba su san cewa suna jawo bata lokaci kan abin da ka iya zame musu bala'i ba ne a gaba."
"Maimakon su bi hanyar da ta dace wajen rushe ginin su yi sabo, mazauna wajen sun gwammace su ci gaba da zama a haka duk da barazanar da ke tattare da shi," in ji Mista Oki.
Shugaban hukumar kula da gine-ginen ya kuma ce wadannan wuraren suna yi wa wadanda ke makwabtaka da su barazana.
Alaba ita ce babbar kasuwar kayan lantarki a Nijeriya.
Sannan ta shahara sosai ba a Nijeriya kadai ba har ma da makwabtan kasashe irin su Ghana da Benin da Togo.