Hukumar NDLEA na yawan yin kamen miyagun kwayoyi a Nijeriya. Hoto/NDLEA

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 5,344.1 a Jihar Legas.

Hukumar ta fara kamen ne a kan hanyar Epe zuwa Lekki inda daga bisani jami’an hukumar da ke aiki a cikin teku suka yi kame a Alpha Beach da ke Jihar Legas.

A sanarwar da hukumar NDLEA ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, jami’an hukumar sun yi kwanton bauna a kan hanyar Epe zuwa Lekki da safiyar Litinin inda suka tare wata babbar mota.

Hukumar ta ce an gano manyan buhunan wiwi da nauyinsu ya kai kilo 2,434.1 a cikin motar.

Hukumar ta ce direban motar ya yi tsalle ya fito daga motar inda ya gudu a cikin wata mota kirar hilux wadda ke yi wa motar wiwin rakiya.

NDLEA ta ce a kamen na biyu, jami’anta da ke aiki a cikin teku ne suka yi shi bayan sun samu bayanan sirri inda suka kama wani jirgin ruwa dauke da tabar wiwin da nauyinta ya kai kilo 2,910 a kusa da bakin ruwan Alpha kafin wanda ya fito daga Ghana.

Hukumar ta ce an kama wasu ‘yan kasar Ghana da suka hada da Monday Saba mai shekara 30 da kuma Hakeem Kwana mai shekara 27.

A Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya kuwa, sanarwar ta ce jami’an na NDLEA sun far wa dajin Ekudo da ke Karamar Hukumar Uhunmwode inda suka lalata sama da kadada biyu ta tabar wiwi.

Hukumar ta ce bayan lalata gonar ta wiwin, sai da ta gano kilo 67 na tabar.

A cewarta, ta kama mutum shida bisa zarginsu da hannu a noman wiwin wadanda suka hada da Onyeka Onyedinma da Monday Onyedi da Alex Eboh da Edosa Imariagbe da Godbless Tunde da kuma Godstime Osarobo.

TRT Afrika