Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta ce ta kama jami’an coci biyu kan zargin safarar miyagun kwayoyi a birnin Warri na Jihar Delta.
Hukumar ta NDLEA ta ce mutum biyun wadanda suka hada da Adewale Abayomi Ayeni mai shekara 39 da kuma Ebipakebina Appeal mai shekara 41 na aiki a Cocin Christ Mercyland Deliverance Ministries.
Ana zargin mutanen suna da alaka da wasu miyagun kwayoyi da aka kama har sau biyu a Delta.
Hukumar ta ce Adewale na daga cikin wadanda ke kula da cibiyar addu’o’i ta cocin sa’annan Ebipakebina ke da alhakin tarbo baki da suka zo daga kasashen waje a filin jirgin sama zuwa cocin.
Baya ga haka kuma, NDLEA din ta ce ta kai samame wani kamfani da ake hada wani lemo na kayan maye a Ajaka Sagamu inda har aka kama wani da ake zargi mai suna Adekunle Adekola.
Kayan mayen wanda ake kira da “skuchies”, lemo ne wanda ake hadawa da miyagun kwayoyi da suka hada da wiwi da barasa.
“Abubuwan da aka gano daga harabar kamfanin sun hada da: Kilo 10 na wiwi da lita 1,356 na skuchies, da lita 20 na codeine da firiza bakwai, da janareto kirar firman da kuma tukunyar gas biyu da sauransu,” in ji sanarwar NDLEA.
Haka kuma hukumar ta ce a Jihar Legas ta kama wani mutum mai suna Segun Odeyemi wanda aka kama shi da manyan buhuna 89 na tabar wiwi nau’in skunk.
An kama shi da wiwin ne a cikin wata babbar motarsa inda nauyin tabar ya kai kilo 3,842.
Safarar miyagun kwayoyi babbar matsala ce a Nijeriya duk da irin samame da kuma kamen da hukumar ta NDLEA take yi.
Ko a kwanakin baya sai da ta kama tirela biyu ta tabar wiwi a Legas da kuma kwayar da za a kai Ingila ta kusan naira miliyan 500.