A ranar Talalta kasashe irin su Njeriya za su kwashe 'ya'yansu daga Sudan/Hoto: Anadolu

Nijeriya da Ghana sun bayyana shirinsu na kwashe ‘yan kasarsu daga Sudan, ta hanyar amfani da kasashe makwabta.

Kasashen Afirka suna fafutukar ceton ‘yan kasashensu daga Sudan, inda matsanancin yaki ke gudana tsakanin sojin kasar da rundunar RSF, don neman iko da birnin Khartoum.

Kasashen sun shiga sahun tarin kasashen duniya da suke ta aikin kwashe ma’aikatan diflomasiyya, da sauran mutanensu ta jiragen ruwa da jiragen sama, tun ranar Asabar.

Arangamar tsakanin rundunonin biyu a Sudan ta janyo mutuwar daruruwan mutane, tare da raunata dubbai.

Nijeriya da Ghana sun ce suna aiki kan wani shiri da zai kai ga dauke ‘yan kasarsu ta cikin kasashen da ke makwabtaka da Sudan.

Nijeriya ta ce tana shirin kwashe mutum 5,500, yawancinsu dalibai, ta titi zuwa kasar Masar. Gwamnatin kasar ta bayyana zabin amfani da titi, sakamakon hadarin amfani da jirgin sama a Sudan.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya ce za a fara kwashewar da zarar gwamnatin Sudan ta ba su tabbacin tsaro da samar da hanyar fita mai aminci.

Ya ce wasu ma’aikatan diflomasiyya za su ci gaba da zamowa a Khartoum don shirya ceton mutane, yayin da ofishin jakadancin ya bayar da shawara ga dalibai da su zauna a gidajensu.

“A zahiri, abin yi a irin wannan yanayi shi ne samar da wata magama da kowa zai hallara kafin a fara aikin kwashe mutane”.

Onyeama ya fada wa ‘yan jaridu ranar Lahadi cewa, “Zabin kadai da ya rage mana shi ne amfani da titunan mota. Amma tabbas ba wai tana da tsaro gabadaya ba, don haka ake bukatar gwamnati ta samar da wata hanya mai tsaro”.

Ita ma Ma’aikatar Harkokin Waje ta Ghana ta ayyana cewa, "Wani adadi na ‘yan kasar, musamman dalibai, rikicin ya shafe su, amma dai an ce suna cikin aminci".

Ma'aikatar kuma ta bayyana cewa ofishin jakadancin kasar a Masar yana aiki kan fitar da ‘yan kasar zuwa Habasha.

A wata sanarwa, ma’aikatar ta fada wa dangi da abokan ‘yan Ghana da suka makale a Sudan, cewa, “Ana yin kokari don tabbatar da tsaron ‘yan uwansu har su iso gida Ghana”.

A yanzu kusan intanet ta dauke baki daya a Sudan, kamar yadda kungiyar nan mai sa-ido kan intanet a duniya, Netblocks ta fada ranar Litinin.

Netblocks ta ambaci wani zargi daga sojin kasar mai cewa rundunar RSF ne suka kassarar harkar sadarwar.

Da yawa daga ‘yan Afirka farar hula da dalibai da suka makale a Sudan, sun dogara ne kan intanet don tuntubar ma’aikatan jakadanci da kuma danginsu da ke gida.

Wannan rikici ya shafi ayyuka a babban filin jiragen sama na birnin Khartoum, inda aka lalata jiragen farar hula, kuma aka lahanta akalla titin jirgi guda. An kuma lalata wasu filayen jirgin sama da ke kasar.

TRT Afrika da abokan hulda