Tsakanin shekarar 1976 da 1989, Nijar da wasu ƙasashen Yammacin Afirka sun gudanar da wani shiri na musamman ta hanyar amfani da maganin ƙwari domin daƙile yaɗuwar cutar. / Hoto: WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar da cewa Jamhuriyar Nijar ta zama ƙasa ta farko a nahiyar Afirka da ta kawar da cutar makantar da ƙuda ke haddasawa wadda aka fi sani da River Blindness.

Nijar ta “zama ƙasa ta biyar a duniya kuma ta farko a Afirka da WHO ta amince cewa ta dakatar da yaɗuwar Onchocerca volvulus,” kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana inda take nufin tsutsar da ke jawo makantar.

Tsakanin shekarar 1976 da 1989, Nijar da wasu ƙasashen Yammacin Afirka sun gudanar da wani shiri na musamman ta hanyar amfani da maganin ƙwari domin daƙile yaɗuwar cutar.

Sai kuma tsakanin 2008 da 2019, an rinƙa bayar da magunguna ga jama’a domin ƙara daƙile bazuwar cutar.

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya jinjina wa Nijar game da ceto jama’ar ƙasar daga wannan cuta wadda ke wahalar da jama’a musamman talakawa.

AFP