A watan Yuli ne Nijar za ta cika shekara guda bayan juyin mulkin 2023. / Hoto: AFP Archive

Aƙalla sojojin Nijar 20 ne suka hallaka, yayin da guda tara suka jikkata bayan wani harin ta'addanci da ya aka kai a yammacin ƙasar. Hukumomin ƙasar sun sanar da fara makokin kwanaki uku don alhinin rasuwar dakarun nasu.

Gwamnatin Nijar ta ce wata "gamayyar ƙungiyoyin 'yan ta'adda" ce ta kai harin ranar Talata, wanda kuma ya rutsa da wani farar-hula wanda shi ma ya rasa ransa.

Wata sanarwa ta Ma'aikatar Tsaron ƙasar ta ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safe agogon Nijar, lokacin da aka kai wa wata tawagar rundunar tsaro hari a ƙauyen Tassia na yankin Tillaberi, wanda ke da iyakoki da ƙasashen Benin da Burkina Faso da Mali.

Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta sanar da makokin kwanaki uku da za a fara daga ranar Laraba, inda tutar ƙasar za ta kasance ƙasa-ƙasa.

Ma'aikatar ta ce daga baya sojoji sun ƙaddamar da wani hari wanda ya kawar da tarin 'yan ta'adda kuma ya lalata abin hawansu.

A saƙonsa na ta'aziyya, Ministan tsaron ƙasar, Laftanar Janar Salifou Mody ya bai wa al'ummar ƙasar tabbacin “jajircewar rundunonin tsaro wajen ci gaba da yaƙi don kare martabar ƙasar.”

Yankin na Tillaberi, wanda ke da iyaka da Burkina Faso da Mali, yana fuskantar hare-hare a-kai-a-kai waɗanda ake ɗora alhakinsu kan ƙungiyoyin ta'addanci na Daesh/ISIS.

Nijar na ƙarƙashin mulkin sojin da suka hamɓarar da gwamnatin farar-hula ta Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli, kuma sojin sun ba da uzurin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

A farkon shekarar nan, gwamnatin sojin ta soke yarjejeniyar haɗin-kan tsaro da ƙasar ta ƙulla da Amurka a 2012 “ba tare da ɓata lokaci ba”.

AA