Gwamnatin Nijar ta ƙwace lasisin aikin ƙungiyar ba da agaji mai zaman kanta ta Faransa, ACTED.
Dokar hana aikin da ƙaramin ministan cikin gidan ƙasar ya sanya wa hannu ranar Talata ta kuma hana ƙungiyar Action Pour le Bien-Être (APBE) aiki a cikin ƙasar.
Duk da cewa gwamnatin ƙasar ba ta bayyana dalilin da ya sa ta hana ƙungiyoyin ci gaba da aiki a Nijar ba, manazarta na ganin matakin ba zai rasa nasaba da ƙokarin da mahukunta a ƙasar ke yi na daɗa saka ido kan harkokin ƙungiyoyin ba da agaji a ƙasar domin inganta tsaro ba.
ACTED, wata ƙungiyar Faransa mai zaman kanta da aka kafa a shekarar 1993, ta fara aiki a Nijar ne tun shekarar 2010 inda ta mayar da hankali yankunan Tillabéry da Diffa da Tahoua da kuma Yamai, yankunan da suka yi fama da rikicin ƴan bindiga.
Ƙungiyar ta bai wa sama da mutum miliyan ɗaya agajin gaggawa da kuma shirye-shiryen ci-gaba mai ɗorewa.
Sai dai kuma tun shekarar 2021 ne zarge-zarge suka ɓata wa ƙungiyar suna a ƙasar. A wancan lokacin, gwamnan Diffa ya dakatar da ayyukan ƙungiyar na wucin gadi yana mai ishara ga “ayyukan da ke janyo zargi da kuma zagon ƙasa " tare da harkar kasuwanci a cikin ƙungiyar.
Ana ganin wancan zargin ka iya taka rawa a wannan dakatarwar da aka yi wa ƙungiyar.
A nata ɓangaren kuma, ƙungiyar mai zaman kanta Action Pour le Bien-Être (APBE), wadda aka kafa a shekarar 2009, ta mayar da hankali ne kan yaƙar tamowa da kare hakkin ɗan'adam da kuma ci-gaban makiyaya. Ta kuma yi aiki wajen samar da abinci da kuma kiwon lafiya
Ƙwace lasisin aikin ƙungiyoyin biyu ya zo ne a lokacin da gwamnati ta matsa ƙaimi wajen sa ido kan ƙungiyoyin masu zaman kansu a Nijar inda hukumomi ke ƙoƙarin tattabatar da aniyarsu ta ƙara sa ido kan ayyukan sakai na ketare da na cikin gida.