Matakin na zuwa ne bayan Rasha ta dakatar da yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine. Hoto/Reuters

Ma’aikatar Kasuwanci ta Jamhuriyar Nijar ta haramta fitar da gero da shinkafa da shansherar shinkafa.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce ta dauki matakin ne domin tabbatar da cewa an samu wadatuwar abinci a kasar.

A sanarwar, ministan kasuwancin na kasar Alkache Alhada ya bukaci jami’an ma’aikatarsa da na hukumar hana fasa-kwauri da jami’an tsaro da su kama sannan su hukunta duk wanda suka kama da laifin fitar da wadannan kayayyaki.

Ana ganin wannan matakin da Nijar ta dauka na da nasaba da matakin da Rasha ta dauka na dakatar da yarjejeniyar fitar da hatsi.

Haka kuma ana ganin rashin tabbaci kan yiwuwar wadatar abinci sakamakon sauyin yanayi da barazanar tsaro a kasar musamman a yankunan da ake da manoma ya sa gwamnatin kasar daukar wadannan matakai.

Yankuna irin su Tillaberi da Diffa da Maradi sun dade suna fuskantar matsalolin tsaro lamarin da ya ja mutane da dama suka rabu da muhallansu ciki har da manoma.

Haka ma makwabtan Nijar kamar Burkina Faso da Jamhuriyyar Benin sun dauki matakai domin dakile duk wata barazana da za ta jawo matsala ko kuma hauhawar farashin abinci.

Nijar na daga cikin kasashen duniya da suka fi noma gero inda take samar da sama da tan miliyan uku a duk shekara.

TRT Afrika