Nijar da Mali da Burkina Faso sun ce babu wanda ya isa ya tilasta musu ci gaba da zama a cikin ƙungiyar ECOWAS har tsawon shekara ɗaya./Hoto:Ofishin shugaban kasar Nijar

Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ranar Laraba sun sanar cewa nan-take suka fice daga ECOWAS, kuma ba za su yi biyayya ga dokokin ƙungiyar da suka buƙaci a su bayar da sanarwar shekara ɗaya kafin su fita daga cikinta ba.

Sun bayyana haka ne kwanaki goma bayan sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ta ƙasashen Yammacin Afirka.

Ranar 28 ga watan Janairu ne ƙasashen uku suka sanar da ficewarsu daga ECOWAS sannan suka aika mata da takardar sanarwar fitarsu washegari.

Doka mai lamba 91 ta ƙungiyar ta tanadi cewa dole ne ƙasar da ta bayyana fitarta daga cikin ECOWAS ta jira tsawon shekara guda kafin ta fita bayar ta bayar da sanarwa a hukumance.

Sai dai ƙasashen uku waɗanda sojoji ke mulka, sun je ba za su jira tsawon shekara ɗaya kafin su kammala fita daga ƙungiyar ba.

"Yanzu gwamnatin Jamhuriyar Mali ba ta cikin yarjejeniya mai lamba 91," in ji wata wasiƙa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar da ke Bamako ta aika wa ECOWAS.

Wasiƙar ta ce ECOWAS, wadda aka kafa a shelarar 1975, ta "taka dokar" da ta kafa ta sakamakon rufe iyakokin Mali a 2022, inda ta hana ta samun damar yin amfani da teku.

Su ma hukumomin Nijar sun tabbatar da ficewarsu daga ƙungiyar nan-take a wata wasiƙa da suka aike mata a makon jiya, inda suka ce yarjejeniya mai lamba 91 ba ta da amfani, a cewar wata majiya ta gwamnatin ƙasar a hirarta da AFP.

Kazalika ma'aikatar harkokin wajen Burkina Faso, a wata wasiƙa makamanciyar ta sauran ƙasasshen biyu da ta aika wa ECOWAS, ta jaddada cewa "ba za mu sauya aniyarmu na fita daga ƙungiyar nan-take ba.

AFP