Juyin mulki na baya-bayan nan a Nijar an yi shi ne a ranar 26 ga watan Yuli. Hoto/AFP

A makon da ya gabata, shugabannin kungiyar ECOWAS sun bayar da umarni ga dakarunsu, kan su tsaya cikin shirin ko-ta-kwana, domin mayar da kasar Nijar kan tsarin dimokuradiyya.

A lokacin taron, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu wanda shi ne shugaban na ECOWAS ya jaddada cewa diflomasiyya ita ce ginshikin tunkarar juyin mulkin Nijar. Sai dai matakin da kungiyar ta dauka na saka batun amfani da karfin soji ya kara dagula lamura.

A lokacin da ECOWAS ke taron nata, sojojin na Nijar sun kafa gwamnatin riko wadanda akasarin mambobinta farar hula ne.

Samun sabuwar gwamnati ba wai alama ce kawai ta raba karfin iko ba, sai dai ta saba wa bukatar ECOWAS da Amurka da Tarayyar Turai, kan batun dawo da Shugaba Bazoum.

ECOWAS a halin yanzu tana wani matsayi inda za ta iya daukar wani mataki, sai dai tambayar ita ce, ko matakin zai zama na diflomasiyya ko na soji ko kuma duka biyu.

Rashin cimma matsayar diflomasiyya

Bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli, ECOWAS ta saka takunkumai kan Nijar, inda ta ba wa sojin kasar mako guda domin mayar da Shugaba Bazoum kan mulki.

A martaninsu, kasashen Mali da Burkina Faso masu makwabtaka da Nijar, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suke adawa da matakin ECOWAS.

Kasashen biyu su ma suna karkashin mulkin soji ne, inda suka ce “duk wani katsalandan na soji kan Nijar za su dauke shi a matsayin kaddamar da yaki kan Burkina Faso ne da Mali”.

A ranar 3 ga watan Agusta wakilan ECOWAS suka isa Yamai babban birnin Nijar a yunkurin sulhu, sai dai wakilan na ECOWAS ba su kwana a kasar ba haka kuma ba su ga shugaban mulkin sojin Abdourahamane Tchiani.

Haka nan, ba su samu ganin Shugaba Mohamed Bazoum ba; wanda wani sakamako ne da ake gani a matsayin na rashin cimma matsayar diflomasiyya.

A ranar, kasar Senegal ta bayyana shirinta na taimakawa duk wani aiki da ECOWAS za ta yi a Nijar.

Sai dai a martanin da sojojin Nijar suka mayar, sun ce “Duk wani hari ko kuma yunkurin kai hari kan Nijar zai fuskanci martani na nan-take daga dakarun Nijar, da na daya daga kawayenta.”

Rikicin na Nijar ya raba kan yankin Yammacin Afirkakan kasashen da suke goyon bayan sojoji da kuma sauran kasashen da ke nuna son amfani da wasu hanyoyi domin dawo da mulkin dimokuradiyya.

Ba zai yiwu a kyale ra’ayin kasashen waje ba kan batun yadda ECOWAS ke sa-ido kan rikicin, da kuma barazanar soji.

Ita ma Amurka ta bayyana goyon bayanta ga ECOWAS da matakanta, inda su kuma sojojin aka ruwaito sun gargadi jami’an diflomasiyyar Amurka kan cewa za a kashe Shugaba Bazoum idan aka yi amfani da soji a kansu.

A karshen mako, masu zanga-zanga da ke gaban ofishin jakadancin Faransa a Yamai sun yi kira da a janye dakarun sojin Faransa daga Nijar.

A tsallaken iyaka a arewacin Nijeriya kuwa, an ga daruruwan masu zanga-zanga da suka hau kan tituna a birnin Kano, suna nuna rashin goyon bayansu ga amfani da karfin soji kan Nijar, inda suka yi kira ga shugabannin da su nemi mafita ta hanyar diflomasiyya.

Rage Tasirin Faransa

Juyin mulkin Nijar shi ne na shida a yankin Sahel, tun daga shekarar 2020. Kuma kamar juyin mulkin da aka yi a Mali da Burkina Faso da Guinea, dalilan hambarar da gwamnatin Nijar sun ta’allaka ne kan rashin jagoranci na gari, da karuwar rashin tsaro da kuma rashin cigaban tattalin arziki.

Haka kuma, wani babban dalili shi ne kin jinin tsaffin kasashen mulkin mallaka, musamman kasar Faransa, wadanda jama’ar kasar Nijar suka kasance karkashin mulkinta tsawon lokaci.

Bugu da kari, kan batun yanayin tsaron yankin, Faransa ta tura sama da dakaru 5,000 a karkashin Operation Barkhane tare da tattara dakaru karkashin rundunar G5-Sahel.

Sannan akwai dakarun rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA da Tarayyar Turai mai rundunar Takuba. Bayan sama da shekaru tara na ayyuka, rikice-rikice da ta’addanci sun karu a yankin.

A Mali mai makwabtaka, an kori dakarun Faransa bayan shekara tara a kasar, inda a Burkina Faso kuma, aka warware wata yarjejeniya da aka cimma a 2018.

Mazauna kasashen sun yi murnar korar sojojin na Faransa, inda kuma ake samun karin goyon bayan kasar Rasha.

Haka ma an ga irin wannan nuna goyon bayan a Nijar, inda aka samu da dama wadanda suka goyi bayan gwamnatin sojin. Hakan ya saba da kiraye-kirayen da ake yi daga kasashen waje na mayar da mulkin dimokradiyya.

Nijar tana da muhimmanci matuka ga Turai inda take da arzikin Uranium. Sama da kashi 50 cikin 100 na Uranium din Nijar yana tafiya ga masana'antun nukiliya na Faransa, inda kuma kaso 24 cikin 100 ke tafiya Tarayyar Turai.

Wani abu da bai zo da mamaki ba shi ne bayan juyin mulkin, gwamnatin Faransa ta bayyana karara cewa za ta mayar da martani idan aka “taba muradan Faransa a Nijar”.

Bugu da kari, Nijar na taka muhimmiyar rawa a tsarukan Faransa na yankin Sahel, da ayyukan Amurka da Tarayyar Turai a yankin.

Akwai sansanin jirgin sama na Faransa da Amurka da ke aiki a kasar, da kuma na jirgi mara matuki, wanda hakan ya sa Nijar ta zama babban sansanin AFRICOM da sauran ayyukan sojoji a Yammaci da Arewacin Afirka.

Da wadannan abubuwan da ke kasa, ana tunanin kasashen Turai da yankin Atlantica za su bi duka hanyoyin da suka dace domin mayar da mulkin dimokradiyya a Nijar.

Akwai bukatar a san cewa fargaba ta yi yawa, haka kuma akwai rashin tabbas a Yammacin Afirka.

Sakamakon yadda suke samun goyon baya a cikin gida, da kuma kiraye-kirayen da ake yi na amfani da karfin soji. Kuma akwai yiwuwar sojojin su ci gaba da watsi da bukatun ECOWAS.

Idan ba a cimma wata matsaya ta diflomasiyya da ECOWAS ba, akwai yiwuwar barkewar yaki a yankin.

Idan ana so a guje wa wannan lamari, sai an samu sadaukarwa daga duka kasashen ECOWAS da sauran shugabannin gwamnati da ke Yamai.

A dayan bangaren, ‘yan Afirka da ke yankin sun fi damuwa kan batun tsaro da kuma matsalar tattalin arziki.

Akwai kuma bukatar a san da cewa duk da halin da ake ciki a Nijar da sauran kasashen yankin, ‘yan Afrika ba za su so a dauki wani mataki mara hikima ba, wanda zai kara dagula yankin kamar yadda irin lamarin ya faru a Libya da hadin kan NATO.

Marubucin Ovigwe Eguegu, mai sharhi ne kan tsare-tsare a Development Reimagined. Ya fi shahara ne a kan siyasar yankuna musamman na Afirka a yadda take sauyawa a duniya.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya gabatar ba sa wakiltar ra'ayoyi da manufofin TRT Afrika.

TRT Afrika