Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta bayar da umarni ga manyan kamfanonin da ke haɗa magunguna da masu sayar da su kan sari da su daina kai magunguna Kasuwar Sabon Gari da Niger Street da ke Birnin Kano.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce hakan ya biyo bayan umarnin da kotu ta bayar na ƙarshe wanda ya ce masu sayar da magunguna su tashi daga Sabon Gari da Niger Street zuwa yankin Dangwauro da ke wajen Kano.
Hukumar ta yi gargaɗi kan cewa duk wani kamfanin da aka kama yana kai magunguna a Sabon Gari Ko Niger Street maimakon Dangwauro wanda nan ne halastaccen wurin da gwamnati ta amince da shi, zai iya rasa lasisinsa.
NAFDAC ta gargaɗi masu shagunan sayar da magunguna da asibitoci da su kula da wannan gargaɗin da ta yi.
Hukumar ta jaddada cewa ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa an daƙile yaɗuwar jabun magunguna ko kuma waɗanda ba su da nagarta.
An daɗe ana zargin masu sayar da magunguna a Sabon Gari da Niger Street da sayar da jabun magunguna da kuma amfani da wuraren domin ɓoye jabun magunguna.