Shugaban kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Binance reshen Afirka ya tsere daga hannun jami’an tsaron Nijeriya.
Ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro ne ya tabbatar da tserewarsa a wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.
Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya, shi ne manajan Binance a yankin Afirka, ya kuma tsere ne daga wurin da yake tsare a ranar Juma’a, kamar yadda sanarwar da Zakari U. Mijinyawa, mai magana da yawun ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro ta tabbatar.
Haka kuma ta ce jami’an tsaron Nijeriya na aiki da ƴan sandan ƙasa da ƙasa domin samun takardar sammacin wadda za ta kai ga kama Mista Anjarwalla.
Wanda ake zargin ya tsere ne bayan kotu ta bayar da umarnin tsare shi tsawon mako biyu inda aka saka ranar 4 ga watan Afrilun 2024 domin ya sake hallara a gaban kotu.
A sanarwar, gwamnatin Nijeriyar ta buƙaci ƴan ƙasar da kuma ƙasashen waje kan duk wani mai ƙarin bayani dangane da wanda ake zargin ya taimaka wa jami'an tsaro.
A watan jiya ne jami'an tsaron Nijeriya suka tsare biyu daga cikin shugabannin Binance, ciki har da Nadeem Anjarwalla.
Shugabannin Binance ɗin sun je Nijeriya ne bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe manhajar.
An tsare shugabannin na Binance ne saboda sun kasa ba da gamsassun bayanai kan yadda manhajar take hada-hadar kuɗi a Nijeriya.
A wancan lokacin, wata majiya a fadar shugaban Nijeriya ta tabbatar wa TRT Afrika cewa manyan batutuwa uku ne suka damu gwamnatin ƙasar kan hada-hadar Binance a ƙasar.
Na ɗaya, kamfanın bai yi rajista da hukumomin ƙasar ba, sannan gwamnati ba ta samun haraji daga ɗimbin ribar da Binance ke samu daga hada-hadar da yake yi a ƙasar, matakin da ke yin illa ga tattalin arzikinta.
Na biyu, babu gamsassun bayanai kan adadin ƴan Nijeriya da ke hulɗa da Binance da kuma yawan kuɗin da ake hada-hadar su.
Na uku, gwamnatin Nijeriya na zargi cewa masu aikata laifukan da suka shafi harkokin kuɗi da masu neman kuɗin fansa suna amfani da manhajar wajen musayar kuɗaɗe ba tare da wata kafa ta iya bibiyarsu don gano abubuwan da suke yi ba.