Mutum uku sun rasu, 49 sun jikkata bayan jiragen ƙasa biyu sun yi karo a Masar

Mutum uku sun rasu, 49 sun jikkata bayan jiragen ƙasa biyu sun yi karo a Masar

Lamarin ya faru ne a Zagazig, mai nisan kilomita 80 daga Alkahira babban birnin na Masar.
Mutum miliyan 105 a Masar sun dogara ne kan sufurin jirgin ƙasa, sai dai layin dogon ya sha fama da hatsari a baya-bayan nan. / Hoto: AA

Ma'aikatar lafiya da kafofin yada labarai na kasar Masar sun sanar da cewa, yara biyu na daga cikin mutane uku da suka mutu a lokacin da wasu jiragen kasa biyu suka yi karo a ranar Asabar a arewacin Masar.

Wannan dai shi ne karo na baya-bayan nan a jerin munanan haɗurran da suka afku a babban layin dogo na kasar Masar, wanda ke fama da yanayi na tsufa da kuma rashin rashin kula.

Wasu mutum 49 kuma sun jikkata a hatsarin, wanda ya afku a garin Zagazig mai tazarar kilomita 80 daga arewacin birnin Alkahira, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana a shafinta na Facebook.

Jaridar Al-Ahram mallakar gwamnati ta ce akwai yara biyu daga cikin wadanda suka mutu.

Yawan samun haɗura

Ministan Sufuri Kamel el-Wazir yayin wata tattaunawa ya bayyana cewa musabbabin wannan karon shi ne "abin da ya shafi dan Adam, amma mun bar wa jami'an tsaro don su tantance", ya kara da cewa babu wata matsala ta fasaha.

Al'ummar Masar miliyan 105 sun dogara kacokan kan zirga-zirgar jiragen kasa, sai dai layukan dogon- daya daga cikin mafi girma a nahiyar Afirka - sun sha fama da munanan hadurra akai-akai.

A cikin 2021, haɗura biyu a cikin ƙasa da wata guda sun kashe fiye da mutum 40.

AFP