Aƙalla mutum tara suka rasa rayukansu sannan huɗu kuma suka jikkata sakamakon mummunar arangama tsakanin jama’ar wani ƙauye da wasu Fulanin wata ruga a Jihar Jigawa, kamar yadda ‘yan sanda a jihar suka tabbatar.
Lamarin ya faru ne bayan wasu ɓarayi waɗanda ake zargin Fulani ne suka fasa wani shago a ƙauyen Gululu da ke Ƙaramar Hukumar Miga inda suka kwashe zobo da wasu kayayyakin cikin shagon, kamar yadda sanarwar mai magana da yawun ‘yan sanda reshen Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ta bayyana.
Domin mayar da martani kan lamarin, sai wasu daga cikin jama’ar ƙauyen suka bi sawun ɓarayin zuwa wata rugar Fulani da ke ƙauyen Yankunama da ke Ƙaramar Hukumar Jahun.
“Ko da suka isa rugar, sai Fulanin suka far musu inda suka rinƙa harbinsu da kwari da baka wanda hakan ya jawo mutum huɗu suka jikkata,” in ji sanarwar.
“Lamarin ya ƙara ƙamari a lokacin da jama’ar ƙauyen suka haɗu sannan suka cinna wa gidajen Fulanin wuta a wurare daban-daban a ƙananan hukumomin Miga da Jahun,” in ji DSP Lawan.
An tura tawagar ‘yan sanda daga reshen Miga da Jahun domin samar da zaman lafiya.
“Ko da samun rahoton, jami’anmu sun garzaya wurin da lamarin ya faru. Abin takaici, an gano gawarwaki tara,” in ji DSP Adam.
"An kai gawarwakin zuwa asibitocin Jahun da Miga, inda jami'an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu."