An kashe fiye da mutum 12,000 sannan aka jikkata sama da mutum 33,000 sakamakon yakin da bangarori biyu suka kwashe wata da watanni suna fafatawa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya./Hoto:AFP

Mutum 250,000 zuwa 300,000 ne suka tsere daga gidajensu a jihar Al Jazirah da ke Sudan tun daga 15 ga watan Disamba sakamakon arangama tsakanin dakarun Rapid Support Forces [RSF] da sojojin Sudan, in ji Hukumar Kula da Masu Kaura ta Majalisar Dinkin Duniya [IOM].

IOM ta fitar da sanarwar ce ranar Litinin bayan ganau sun ce dakarun RSF sun shiga Wad Madani, birni na biyu mafi girma a Sudan, wanda ke cike da 'yan gudun hijira kuma inda mutane ke samun taimako daga yakin da aka kwashe wata takwas ana gwabzawa a kasar.

Bidiyoyin da dakarun RSF suka wallafa sun nuna mayakansu a cikin motocin a-kori-kura a kan titunan Wad Madani da kuma kan gadoji na yankin Blue Nile inda suka kwashe tsawon lokaci suna fafatawa da dakarun gwamnati. Ganau sun ce dakarun na RSF sun kai samame wasu kauyuka da ke yankin.

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya yi kira ga bangarorin biyu su yi gaggawar tsagaita wuta sannan su zauna a teburin sulhu domin sake gina kasar Sudan.

An kashe fiye da mutum 12,000 sannan aka jikkata sama da mutum 33,000 sakamakon yakin da bangarori biyu suka kwashe wata da watanni suna fafatawa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Kimanin mutum miliyan 25 ne suke bukatar agajin jinkai, wato rabin al'ummar kasar kenan.

Kusan mutum miliyan 7 ne suke gudun hijira ko dai a cikin Sudan ko kuma a kasshe da ke makwabtaka.

TRT Afrika da abokan hulda